Buhari: An samu mummunar baraka tsakanin Babagana Munguno da Abba Kyari

Buhari: An samu mummunar baraka tsakanin Babagana Munguno da Abba Kyari

Mun samu labari cewa an samu sabani tsakanin wasu Jiga-jigai a gwamnatin Buhari, inda NSA Babagana Monguno ya ke zargin Abba Kyari da yin ba-ba-kere a fadar shugaban kasa.

Janar Babagana Monguno mai ritaya ya na zargin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, da shiga tsakanin wasu Jami’an gwamnati da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Jaridar Premium Times ce ta fitar da wannan rahoto na musamman a Ranar Litinin, 17 ga Watan Fubrairun 2020. Abin har ta kai Babagana Monguno ya nemi a daina sauraron Abba Kyari.

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkar tsaron, ya rubutawa Shugabannin Hafsun Soji takarda su daina daukar umarni daga ofishin Abba Kyari wanda ake ganin ya na wuce gona da iri.

NSA Monguno ya na zargin cewa Abba Kyari ya na aikawa Hafsun Sojoji umarni ba tare da yarda ko sanin shugaban kasa ba, ana sa tunanin, wannan ya taimaka wajen tabarbarewar tsaro.

Buhari: An samu mummunar baraka tsakanin Babagana Munguno da Abba Kyari
An samu sabani tsakanin COS Abba Kyari da NSA Babagana Munguno
Asali: UGC

“Shugaban ma’aikatan gidan gwamnati ba shugaban kwamitin tsaro ba ne, haka zalika babu wanda ya rantsar da shi domin ya kare Najeriya.” Manjo Janar Munguno ya rubuta.

“A dalilin haka, jagorantar zama da shugabannin hafsun sojoji da manyan jami’an tsaro da kuma Jakadun kasa ba tare da NSA da Ministoci ba, raina ofishin shugaban kasa ne.” Inji NSA.

Janar Munguno mai ritaya ya na da ra’ayin cewa bai kamata Kyari ya rika shugabantar zama a madadin shugaban kasa ba, NSA din ya ke cewa wannan ya sabawa doka da tsarin kasa.

An dade ana zargin Abba Kyari da yin ba-ba-kere a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari. Masu magana da yawun shugaban kasa sun ki maida martani game da zargin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel