APC: Babachir Lawan ya bayyana babbar illar da Oshiomhole ya yi wa arewa

APC: Babachir Lawan ya bayyana babbar illar da Oshiomhole ya yi wa arewa

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal ya kwatanta jam'iyyarsa ta APC a matsayin kungiya mai cike da abubuwan ban dariya.

A yayin zantawa da manema labarai, Lawal ya ce Adams Oshiomhole, shugaban jam'iyyar APC ta kasa da magoya bayansa ne suka dakatar da Lawal Shaibu, mataimakin shugaban jam'iyyar na Arewa da kuma Inuwa Abdulkadir, mataimakin shugaban jam'iyyar na Arewa maso yamma.

Akwai tsama tsakanin Shaibu da Oshiomhole kafin a dakatar dashi yayin da aka zargi Abdulkadir da rashin goyon bayan jam'iyya kafin a dakatar da shi, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Tsohon sakataren gwamnatin tarayyar ya ce abinda Oshiomhole yake yi sun samo asali ne daga yadda 'yan jam'iyyar na Arewa suka yi watsi da damarsu ta zaben shugabanni a jam'iyyar.

"Jam'iyyar APC abin dariya ce. A yanzu haka da muke magana, shugaban jam'iyyar da masu masa biyayya sun dakatar da mataimakin jam'iyyar na Arewa. Shugaban jam'iyyar na Arewa kenan fa gaba daya. Arewa wacce ta fi ko wanne yanki girma," ya ce.

APC: Babachir Lawan ya bayyana babbar illar da Oshiomhole ya yi wa arewa
APC: Babachir Lawan ya bayyana babbar illar da Oshiomhole ya yi wa arewa
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Sabbin masarautu: Kotu ta yi watsi da karar masu hannu a nada sabon Sarki

"Sakataren jam'iyyar na kasa wanda dan Arewa ne ya zama gwamnan jihar Yobe. A halin yanzu babu wani kwakwaran zance na wanda zai maye gurbinsa. Kusan shekara daya cif kenan, babban yankin na kasar nan ba shi da wakili a jam'iyyar koda kuwa yayin yanke hukunci ne." Ya kara da cewa.

Lawal ya ce Oshiomhole ba ya saka mambobin kwamitin aikin jam'iyyar na kasa kafin ya yanke hukunci.

"Ina da kusanci da mambobin kwamitin aikin jam'iyyar na kasa. Suna yawan korafi a kan yadda yake waresu wajen yanke hukunci. Ba shugaban jam'iyya kadai ke yanke hukunci ba, kamata yayi a ce yana shawara da zababbu." Ya ce.

"Wannan na daga cikin amfanin mataimakan shugabannin jam'iyyar wadanda suka fito daga yankuna daban-daban. Akwai bukatar yankunan wadanda su kadai suka sani kuma zasu iya sanar da su kafin a zartar da hukunci. Idan har kuwa ba a sauraronsu yayin yanke hukunci, toh kuwa an danne musu wasu hakkokinsu." in ji shi.

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya din yana mamakin abinda kwamitin sasanci na jam'iyyar wanda Bisi Akande ke jagoranta zai cimma wa.

Kamar yadda ya ce, zai fi idan 'yan siyasa suka rungumi kaddararsu tare da jinyar raunikan baya a kan wani sasanci.

"A siyasa, sau da yawa babu amfani sasanci. Dole ne wani yayi rashi ai," ya ce.

Lawal ya ce duk da Oshiomhole na iya bakin kokarin shi amma akwai bukatar a gyara jam'iyyar.

Har yanzu dai Simon Egbebulem, mai magana da yawun Oshiomhole din bai yi martani a kan wannan maganar ta Lawal ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel