Ya zama dole a sallami shugabannin tsaro – Yan majalisar tarayya

Ya zama dole a sallami shugabannin tsaro – Yan majalisar tarayya

Wata kungiyar yan majalisar tarayya karkashin inuwar Young Parliamentarians Forum (YPF) na majalisar wakilai, a jiya Lahadi, 16 ga watan Fabrairu, ta bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tsige shugabannin tsaro.

A cewar kungiyar, akwai bukatar hakan don magance hauhawan rashin tsaro a Najeriya.

Kungiyar ta yi wannan kiran ne a karshen taronta na shekara a Owerri, jahar Imo.

Yan majalisar, sun ce halin da tsaro ke ciki a yanzu barazana ne ga hadin kan kasa da kuma ci gaban kasar.

Ya zama dole a sallami shugabannin tsaro – Yan majalisar tarayya
Ya zama dole a sallami shugabannin tsaro – Yan majalisar tarayya
Asali: UGC

Kungiyar ta c eta goyi bayan hukuncin majalisar dokokin tarayya da ke kira ga tsige shugabannin tsaron kasar cikin gaggawa.

Ta yi kira ga gwamnatoci a dukkan matakai da su sake duba halin da tsaron kasar ke ciki a yanzu don tabbatar da zaman lafiya da tsaro daidai da tsarin tsaro na damokradiyya. Ta kuma yi kira ga Karin shugabanni da kwararru a hukumomin tsaro.

KU KARANTA KUMA: Har yanzu mutanen Borno na son Buhari – Fadar shugaban kasa

A wani labarin mun ji cewa an ji karan harbe harben bindiga a daren Lahadi, 16 ga watan Feburairu a garin Maiduguri yayin da zaratan dakarun rundunar Sojan kasa na Najeriya suka yi musayar wuta da mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram.

Premium Times ta ruwaito da misalin karfe 7:30 na daren Lahadi aka fara musayar wutar a lokacin da yan Boko Haram suka yi kokarin kutsawa cikin garin Maiduguri domin su kaddamar da munanan hare hare.

Sai dai sun ci karo da Sojojin Najeriya, inda aka yi ta kai ruwa rana har kusan tsawon sa’a guda a daidai yankin Muna na garin Maiduguri dake kan babbar hanyar Gamborou-Ngala, wanda hakan ya jefa jama’an yankin cikin halin tsoro da fargaba.

Wani jami’in tsaro na yan sa kai dake yankin, kuma mazaunin sansanin yan gudun hijira na Muna, Ahmadu Haga ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace: “Harin ya faru ne a wani wuri dake kusa da Kaliyari dake can nesa da bayan unguwarmu.”

Haka zalika wani jami’in Civilian-JTF, Bello Dambatta ya bayyana cewa harin ya faru ne a daidain shingen binciken ababen hawa na Sojoji dake kauyan Ngwom.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel