An yi ba ta kashi tsakanin Sojoji da mayakan Boko Haram a garin Maiduguri

An yi ba ta kashi tsakanin Sojoji da mayakan Boko Haram a garin Maiduguri

An ji karan harbe harben bindiga a daren Lahadi, 16 ga watan Feburairu a garin Maiduguri yayin da zaratan dakarun rundunar Sojan kasa na Najeriya suka yi musayar wuta da mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram.

Premium Times ta ruwaito da misalin karfe 7:30 na daren Lahadi aka fara musayar wutar a lokacin da yan Boko Haram suka yi kokarin kutsawa cikin garin Maiduguri domin su kaddamar da munanan hare hare.

KU KARANTA: Maguzawa 200 sun karbi kalmar Shahada a hannun Ganduje a fadar gwamnatin Kano

An yi ba ta kashi tsakanin Sojoji da mayakan Boko Haram a garin Maiduguri
An yi ba ta kashi tsakanin Sojoji da mayakan Boko Haram a garin Maiduguri
Asali: Facebook

Sai dai sun ci karo da Sojojin Najeriya, inda aka yi ta kai ruwa rana har kusan tsawon sa’a guda a daidai yankin Muna na garin Maiduguri dake kan babbar hanyar Gamborou-Ngala, wanda hakan ya jefa jama’an yankin cikin halin tsoro da fargaba.

Wani jami’in tsaro na yan sa kai dake yankin, kuma mazaunin sansanin yan gudun hijira na Muna, Ahmadu Haga ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace: “Harin ya faru ne a wani wuri dake kusa da Kaliyari dake can nesa da bayan unguwarmu.”

Haka zalika wani jami’in Civilian-JTF, Bello Dambatta ya bayyana cewa harin ya faru ne a daidain shingen binciken ababen hawa na Sojoji dake kauyan Ngwom;

“Sun yi kokarin kai ma birnin Maiduguri hari ne, amma bayan sun kai ma shingen binciken hari, amma Allah Yasa Sojoji sun yi bakin kokarinsu wajen fatattakarsu.”Inji shi.

Sai dai Danbatta bai tabbatar da adadin mutanen da suka mutu a sanadiyyar musayar wutan ko suka jikkata ba. Wannan hari ya faru ne a daidai lokacin da yan Boko Haram suka kai ma wani unguwa Babangida hari a jahar Yobe.

Amma mai magana da yawun rundunar Sojan kasa ya tabbatar da cewa Sojoji sun fatattaki mayakan na Boko Haram da suka kai harin Yobe.

A wani labarin kuma, rundunar Sojan sama ta Najeriya ta bayyana rahoton dake yawo a kafafen sadarwa na cewa wai dakarunta sun kashe mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram guda 250, a matsayin labarun kanzon kurege.

Wannan labari ya fara yawo a kafafen sadarwa ne tun a ranar 13 ga watan Feburairu, kuma wai ya fito ne daga wajen wani mutumi mai suna ‘Comr Aminu Shuaibu Musawa, kamar yadda hukumar sojan sama ta bayyana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel