Hare-haren yan bindiga: Shinkafi ya nemi a kama Yari a wata wasika zuwa ga IGP, DSS da sauransu

Hare-haren yan bindiga: Shinkafi ya nemi a kama Yari a wata wasika zuwa ga IGP, DSS da sauransu

- Alhaji Sani Abdullahi Shinkafi, ya yi kira ga a yi gaggawan kama tare da hukunta tsohon gwamnan jahar Zamfara, Alhaji Abdulaziz Yari

- Shinkafi a wani korafi zuwa ga Sufeto Janar na yan sanda, Mohammad Adamu, ya zargi Yari da daukar nauyi da kuma haddasa hare-haren yan bindiga a Zamfara

- Sai dai Yari ya bayyana korafin a matsayin aikin makirai da ke aiki dare da rana don ganin sun halakanta shi da matsalolin tsaro a jahar

Wani jigon jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) a jahar Zamfara, Alhaji Sani Abdullahi Shinkafi, ya yi kira ga a yi gaggawan kama tare da hukunta tsohon gwamnan jahar, Alhaji Abdulaziz Yari.

Shinkafi a wani korafi zuwa ga Sufeto Janar na yan sanda, Mohammad Adamu, ya zargi Yari da daukar nauyi da kuma haddasa hare-haren yan bindiga a Zamfara wanda ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane da kuma jikkata wasu da dama.

Yan bindigan sun kuma halaka gidaje da dama da kuma dukiyoyi na miliyoyin nairori a yankunan jahar da dama.

Hare-haren yan bindiga: Shinkafi ya nemi a kama Yari a wata wasika zuwa ga IGP, DSS da sauransu
Hare-haren yan bindiga: Shinkafi ya nemi a kama Yari a wata wasika zuwa ga IGP, DSS da sauransu
Asali: UGC

Sai dai Yari ya bayyana korafin a matsayin aikin makirai da ke aiki dare da rana don ganin sun halakanta shi da matsalolin tsaro a jahar.

Shinkafi, a korafin, ya yi ikirarin cewa ba da dadewa ba yan bindiga za su tayar da jahar Zamfara idan har ba a kama Yari sannan aka hukunta shi ba. Ya kuma zargi tsohon gwamnan da hada mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jahar fada da gwamnatin jahar.

Mai korafin ya kuma yi zargin cewa akwai shirin da tsohon gwamnan ke yin a hargitsa yarjejeniyar zaman lafiya a aka kulla tsakanin gwamnati da hukumomin tsaro yan makonni da suka gabata ta hanyar amfani da yan bindigar da basu tuba ba.

KU KARANTA KUMA: Tsohon kakakin majalisar dokokin Nasarawa ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa an tura kwafin takardar korafiun Shinkafa zuwa ga Shugaban hafsan soji, Shugaban ma’aikatan tsaro, Shugaban hafsan sopjin ruwa, Shugaban hafsan sojin sama, darakta janar na hukumar DSS da kuma mai ba kasa shawara a harkar tsaro.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel