Tsohon kakakin majalisar dokokin Nasarawa ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

Tsohon kakakin majalisar dokokin Nasarawa ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

- Tsohon kakakin majalisar dokokin jahar Nasarawa, Musa Ahmed Mohammed, ya sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party, (PDP) zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC)

- Hon. Mohammed ya wakilci mazabar Nasarawa sau biyu a majalisar dokokin jahar kuma ya kasance kakakin majalisar dokokin jahar a majalisa ta uku da hudu

- Kakakin majalisar dokokin jahar mai ci, Ibrahim Balarabe Abdullahi, ya bayyana cewa ahlin APC na yiwa tsohon kakakin majalisar maraba da zuwa cikinta

Wani tsohon kakakin majalisar dokokin jahar Nasarawa, Musa Ahmed Mohammed, ya sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party, (PDP) zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Tsohon kakakin majalisar ya janye daga kasancewa dan PDP a cikin wata wasika zuwa ga Shugaban jam’iyyar a karamar hukumar Nasarawa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Idan za a tuna, Hon. Mohammed ya wakilci mazabar Nasarawa sau biyu a majalisar dokokin jahar kuma ya kasance kakakin majalisar dokokin jahar a majalisa ta uku da hudu.

A martaninsa, kakakin majalisar dokokin jahar mai ci, Ibrahim Balarabe Abdullahi, ya bayyana cewa ahlin APC na yiwa tsohon kakakin majalisar maraba da zuwa cikinta.

KU KARANTA KUMA: Murna fal ciki yayinda hazikin dan sanda Abba Kyari ya samu sarauta a Maiduguri

Hakazalika, Shugaban karamar hukumar Nasarawa, Muhammad Sani Otto, ya bukaci tsohon kakakin majalisar da ya bayar da gudunmawa zuwa ga cigaban jam’iyyar dama kasar baki daya.

A wani labarin na daban, mun ji cewa jam’iyyar adawar nan ta PRP ta bayyana shirinta na doke APC da PDP daga kan mulki a babbam zabe mai zuwa da za ayi a Najeriya a shekarar 2023.

Shugaban jam’iyyar PRP na kasa, Alhaji Falau Bello, shi ne ya bayyana shirin jam’iyyar na karbe mulki daga hannun ‘Yan siyasar APC da kuma PDP.

Falalu Bello ya nuna cewa a halin yanzu PRP ta dawo da karfinta, ta kuma shiryawa zaben da za ayi nan gaba. Lokacin tashi kurum ake jira inji Bello.

Alhaji Bello ya yi wannan bayani ne a Garin Kaduna a cikin makon nan, a wajen taron majalisun NEC da NWC da kuma BOT na Amintattun jam’iyyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel