Jirgin yakin Amurka ya fadi a Afghanistan

Jirgin yakin Amurka ya fadi a Afghanistan

Ma'aikatar tsaron Amurka a ranar Litinin ta tabbatar da labarin fadowar jirgin yakinta a yankin Ghazni a kasar Afghanistan amma ta karyata rade-radein cewa yan mayakan Taliban suka baro jirgin

Kakakin Sojin Amurka dake kasar Afghanistan, Kanar Sonny Legget, ya atabbatar da hakan a jawabin inda ya ce jirgin kirar Bombardier E-11A, ne ya fado.

"Yayinda muke gudanar da bincike kan lamarin, babu wasu alamun dake nuna cewa makiya ne suka baro jirgin." Yace

Bai fadi komai kan Sojojin da hadarin ya shafa ba.

Jirgin yakin Amurka ya fadi a Afghanistan
Jirgin yakin Amurka ya fadi a Afghanistan
Asali: Facebook

Mun kawo muku rahoton cewa kimanin Sojojin Amurka dozin uku ne suka samu rauni a kwalkwalwa sakamakon harin ramuwar gayya da kasar Iran ta kai sansanin Sojin Amurka dake Iraqi, hedkwatar Sojin Amurka, Pentagon ta bayyana ranar Juma'a.

Kakakin Pentagon, Jonathan Hoffman, ya bayyanawa manema labarai cewa: "Jimillar Sojoji 34 da aka gwada suna fama da rauni a kwakwalwa."

Da farko, shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa babu sojan Amurkan da aka rasa a harin da Iran ta kai sansanin Sojin Amurka ranar 7-8 na Junairu.

Daga baya hukumomi suka bayyana cewa Sojin Amurka 11 sun jikkata.

Amma a yanzu, Hoffman ya ce bayan harin, an kai Sojoji 17 kasar Jamus domin jinya kuma takwas cikinsu sun dawo Amurka ranar Juma'a.

An fara rikici ne tsakanin Amurka da Iran ranar da Kasar Amurka ta kai mumunan harin jirgin sama domin hallaka babban kwamandan kasar Iran, Qassem Soleimaini da kwamandan rundunar Kata’ib Hezbollah na Iraqi, Abu Mahdi Muhandis.

Hedkwatan hukumar Sojin Amurka, Pentagon, ta tabbatar da hakan a jawabin da ta saki cewa lallai harin Amurka ya kashe kwamandan rundunar Al-Quds na Iran, Qassem Soleimani, a filin jirgin saman Baghdad dake Iraq.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Asali: Legit.ng

Online view pixel