Zazzabin cutar lassa: Likitoci 7 da ma’aikatan jinya 5 na cikin tsaka mai wuya a jahar Adamawa

Zazzabin cutar lassa: Likitoci 7 da ma’aikatan jinya 5 na cikin tsaka mai wuya a jahar Adamawa

Likitoci bakwai da ma’aikatan jinya biyar ne suke karkashin kulawa bayan an kebancesu a cibiyar kiwon lafiya na gwamnatin tarayya dake garin Yola, babban birnin jahar Adamawa, sakamakon sun yi mu’amala da mutanen dake dauke da cutar zazzabin Lassa.

Jaridar The Cable ta ruwaito wata mata mai dauke da juna biyu ne take dauke da cutar, sai dai bata samu nasarar haihuwa ba, inda ta yi barin cikinta, jami’an kiwon lafiya sun kamu da cutar ne a lokacin da suka kwantar da ita a sashin haihuwa, inda suka cire mahaifarta.

KU KARANTA: Allah kare: Zazzabin beraye ‘Lassa’ ya halaka mutane 4 a jahar Taraba

“Bayan an cire mahaifar, sai aka lura ta kamu da zazzabi mai zafi, kuma tana ta zubar da jini, wannan yasa malaman asibitin suka yi zargin ta kamu da cutar zazzabin Lassa, don haka suka kebance ta a wani daki.

“Bayan an kebance ta ne sai aka dauki jininta domin gudanar da gwaje gwaje a kan jinin, amma da yake ba’a gudanar da gwajin a asibitin, don haka sai a ranar Lahadi aka samu sakamakon gwajin wanda ya nuna tana dauke da cutar, amma matar ta rasu kwanaki biyu kafin fitowar sakamakon.

“Har yanzu mutanen da aka kebance basu nuna wani alamana cutar ba, amma likitoci 7, jami’an jinya 5 da wasu ma’aikatan asibitin 2 ne suka yi mua’amala da matar, don haka aka waresu domin sa ido a ga yiwuwar kamuwarsu da cutar na tsawon kwanaki 21.” Inji majiyar.

A wani labarin kuma, cutar zazzabin beraye, watau Lassa Fever ya yi sanadiyyar mutuwar mutane hudu a jahar Taraba tun bayan barkewar cutar a jahar, kamar yadda kwamishinan kiwon lafiya na jahar, Innocent Vakkai ya tabbatar.

Kwamishinan ya bayyana haka ne a ranar Litinin 27 ga watan Janairu a garin Jalingo, inda yace an samu bullar cutar a wurare 15 a jahar, amma mutane 4 ne kawai aka tabbatar da kamuwarsu, yayin da 5 suka mutu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel