Shugaban PDP a jihar Imo ya yi hannun riga da jam'iyyar, ya koma APC

Shugaban PDP a jihar Imo ya yi hannun riga da jam'iyyar, ya koma APC

Shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, na jihar Imo. Charles Ezekwem, ya yi murabus daga kujerarsa, ya yi hannun riga da jam'iyyar kuma ya sauya sheka zuwa jam'iyyar All progressives Congress.

A wasikar murabus da ya aika ranar Litinin a Owerri, Ezekwem ya ce ya yanke shawaran fita daga jam'iyyar ne saboda kalubalen da jam'iyyar ke fuskanta da kuma goyon bayan masoyansa.

Amma wasu rahotanni sun bayyana cewa Ezekwen ya yi murabus ne saboda ana shiryen dakatad da shi a taron gangamin jam'iyyar.

Gabanin murabus din sa, ya kasance shugaban majalisar kungiyar kwallon Heartland Owerri.

Yan majalisar dokokin jihar Imo guda tara sun sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) daga jam'iyyun Peoples Democratic Party PDP, All Progressives Grand Alliance APGA, da Action Alliance.

KU KARANTA: EFCC ta gurfanar da Shehu Sani a kotu

Kakakin majalisar jihar ya bayyana hakan a wasikar da ya karanta a zauren majalisa ranar Talata.

Ga jerin wadanda suka koma APC:

Authur Egwim (Ideato North) AA zuwa APC

Chyna Iwuanyanwu (Nwangele), daga PDP zuwa APC.

Chidiebere Ogbunikpa(Okigwe), daga PDP zuwa APC.

Obinna Okwara(Nkwerre), AA zuwa APC

Paul Emeziem (Onuimo) daga PDP zuwa APC..

Ekene Nnodimele (Orsu) APGA zuwa APC,

Johnson Duru(Ideato South), AA zuwa APC

Ngozi Obiefule (Isu) daga AA zuwa APC

Heclus Okorocha (Ohaji/Egbema) daga PDP zuwa APC.

Mun kawo muku rahoton cewa Mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Imo, Okey Onyekanma, ya yi murabus daga kujerarsa.

Dukkan wannan dambarwan siyasan ya biyo bayan hukuncin kotun kolin Najeriya da ta fititiki gwamnan PDP, Emeka Ihedioha, kuma ta baiwa na APC< Hope Uzodinma.

Kotun kolin ta alanta Hope Uzodinma na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) matsayin zakaran zaben gwamnan 9 ga Maris, 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel