Atiku bai ga laifin kafa Dakarun Amotekun domin inganta tsaro ba

Atiku bai ga laifin kafa Dakarun Amotekun domin inganta tsaro ba

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce babu wata matsala don an kafa jami’an da za su rike tsare jama’a a Jihohi ko Yankin Najeriya.

Atiku Abubakar ya nuna goyon bayansa ga yunkurin da wasu gwamnoni su ke yi na kirkiro jami’an da za su taimakawa gwamnatin tarayya wajen tsare rai da dukiya.

‘Dan takarar shugaban kasar na PDP ya yi wannan jawabi ne ta bakin Mai magana da yawun bakinsa, Mista Paul Ibe a jiya Ranar Lahadi, 19 ga Watan Junairu, 2020.

A jawabin, Atiku, ya bayyana cewa babban hakkin da ke wuyan gwamnati shi ne tsare ran bayin Allah da abin da su ka mallaka don haka ya goyi bayan irinsu Amotekun.

“A wajen sauke wannan nauyi, Jihohi kan dauki matakai da dama da za su yi aiki wajen tsare al’umma. Babu tantama, a ‘yan shekarun nan, ‘Yan sanda sun sha wahala.”

KU KARANTA: Rigima bayan Gwamnan Ekiti ya ce APC za ta iya rugujewa a 2023

Atiku bai ga laifin kafa Dakarun Amotekun domin inganta tsaro ba
Atiku Abubakar ya na goyon bayan Jihohi su kula da sha'anin tsaronsu
Asali: Twitter

Jagoran hamayyar ya kara da cewa: “Zahirin maganar gaskiya ita ce kalubalen da Dakarun ‘Yan Sanda su ke fuskanta zai sa a canzawa tsarin tsaro zani a kasar nan”

“A yanzu a Najeriya, kusan babu wata jiha da ba ta fama da wani yanayi na rashin tsaro”

“A dalilin wadannan mabanbantan matsoli da su ka kebanta da kowane yanki, shiyasa zai yi wahala Dakarun ‘Yan Sandan kasa su iya kawo karshen matsalolin.”

A karshe jawabin ya ce: “Duba da wannan, akwai bukatar kafa karin jami’an tsaro da za su tunkari matsalolin rashin tsaro da ta’adi da mu ke ta kara fama da su.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel