Kotun koli ce karshe, ka rungumi kaddara kawai - Atiku ya bawa gwamnan Imo shawara

Kotun koli ce karshe, ka rungumi kaddara kawai - Atiku ya bawa gwamnan Imo shawara

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar yayi kira ga Emeka Ihedioha da kuma jam'iyyar PDP da su rungumi hukuncin kotun koli na yadda aka shafe nasararsa a zaben shugabancin jihar Imo.

Atiku ya bayyana hakan ne a wata takarda a ranar Laraba wacce tace, "Dangane da hukuncin kotun koli da ta soke zaben dan takarar jam'iyyar PDP, Emeka Ihedioha, a matsayin gwamnan jihar Imo, zan iya cewa tunda kotun kolin ce karshe, dole ne mu karba hukuncinta," Atiku ya wallafa a shafinsa na tuwita.

"Amma kuma, duk da bamu yi tsammanin faruwar hakan ba. Dole ne mu rungumi hukuncin shari'a don kuwa sabanin hankali ce."

A ranar Talata ne kotun koli ta soke nasarar Emeka Ihedioha kuma ta bayyana Sanata Hope Uzodinma na jam'iyyar APC a matsayin gwamnan jihar.

DUBA WANNAN: Kotun koli ta saka sabuwar rana domin yanke hukunci a kan kujerar Tambuwal

Kotun tace karamar kotun tayi kuskure a shari'ar lokacin da ta soke shaidar da aka bayyana a gabanta na cewa kuri'un akwatuna 388 ne ba a saka wa APC da Uzodinma ba.

Kotun ta umarci da a rantsar da Uzodinma a matsayin wanda ya lashe zaben 9 ga watan Maris na 2019 a jihar Imo.

Atiku yayi kira ga Ihedioha da kada ya ja da hukuncin kotun amma "ya dawo da karfinsa".

Atiku yace babban burinsa shine ganin Najeriya ta gyaru a lokacin rayuwarsa. Tabbatar Najeriya a matsayin kasar hadin kai, lumana da cigaba shine fatan dan takarar shugaban kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel