Jita - jitar kafa sabuwar jam'iyya: Atiku ya yi bayani a kan haduwarsa da Tinubu, Osinbajo da Kyari

Jita - jitar kafa sabuwar jam'iyya: Atiku ya yi bayani a kan haduwarsa da Tinubu, Osinbajo da Kyari

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi karin haske a kan haduwarsa da jagoran jam'iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, a Abuja ranar Asabar.

A cewar Atiku, haduwar tasu bata da nasaba, ta kusa ko ta nesa, da siyasa, kawai sun hadu ne a wurin daurin aure.

A ranar Asabar ne shugaban hukumar yaki da rashawa na farko, Nuhu Ribadu a ranar Asabar ya hada manyan 'yan siyasan kasar Najeriya a karkashin inuwa daya.

Dukkansu sun hadu ne masallacin An-Nur dake Abuja a yayin shagalin bikin dan Nuhu Ribadu, Mahmud da matarsa, Amina Aliyu Isma'ila.

An hangi Atiku, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP a zaben 2019, yana hira cikin raha da manyan 'ya'yan jam'iyyar APC yayin halartar daurin auren.

Manyan 'yan siyasan da suka samu halartar wajen bikin sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, jigon jam'iyyar APC Asiwaju Bola Tinubu.

Jita - jitar kafa sabuwar jam'iyya: Atiku ya yi bayani a kan haduwarsa da Tinubu, Osinbajo da Kyari
Atiku da Tinubu
Asali: UGC

Jaridar ripplesnigeria.com ta rawaito cewa wanna shine karo na biyu da aka ga Tinubu da Atiku tare a 'yan kwanakin baya bayan nan.

Da yake magana ta hannun mai taimaka masa a bangaren yada labarai, Paul Ibe, Atiku ya yi watsi da rade - radin da ake yi a kan cewa haduwar tasu tana da nasaba da kulle - kulle irin na siyasa.

DUBA WANNAN: Rayuwa Wani tsohon gwamna na kwance da shanyewar barin jiki, yana neman kudin magani

Ya kara da cewa ba wani sabon abu bane ga manyan 'yan siyasa da 'yan kasuwar dake kasar nan su halarci daurin da ko diyar wanin babba a kasar nan, kamar yadda dukkan manyan kasar nan suka halarci daurin auren dan Atiku da aka yi a Masallacin Sultan Bello dake Kaduna a ranar 14 ga watan Disamba, 2019.

Sauran jiga-jigan da suka halarci taron daurin auren dan Ribadu sun hada da gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari, tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aliyu Wamako, tsohon gwamnan jihar Ogun, Sanata Ibikunle Amosun da kuma lauya mai rajin kare hakkin bil Adama, Femi Falana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel