Safiya Badamasi: Bahaushiya ta farko da ta fara samun matsayin SAN

Safiya Badamasi: Bahaushiya ta farko da ta fara samun matsayin SAN

Safiya Umar Badamasi ce mace bahaushiya musulma ta farko da ta fara kai matsayin babban lauya na kasa (SAN) kuma itace ce ta farko da ta taba kai samun wannan darajar a jihar Katsina.

Tana daya daga cikin lauyoyi 117 da suka nemi samun matsayin a wannan shekarar. Daga bisani ta kasance cikin 80 da aka tattance kuma daga karshe tayi nasarar kasance cikin 38 da aka karrama ta matsayin na SAN a bana.

A hirar da tayi da Daily Nigerian, Safiya Badamasi ta yi murnar kasancewa cikin wadanda suka zamo abin kwatance idan ana batun ilimin 'ya'ya mata musamman a cikin al'uammar musulmi na Arewa.

Ta ce kasancewarta SAN na farko a jihar ta, za ta zauna a Katsina domin bawa sauran lauyoyin da ke tasowa kwarin gwiwa da taimakon da suke bukata domin samun nasara.

DUBA WANNAN: An gano yarjejeniyar da aka kula tsakanin Goje da Shugaba Buhari kafin ya janye takararsa

"Na fi son in tsaya a Katsina domin in bayar da gudunmawa wurin bawa lauyoyi masu tasowa kwarin gwiwa a maimakon in tafi wani wuri saboda kudi," inji ta.

An haifi ta a ranar 12 ga watan Yunin 1968 a garin Malumfashi da ke jihar Katsina, inda ta fara aiki har ta kai matsayin babban mai shari'a na jihar/famanen sakatare a Ma'aikatar Shari'a na jihar Katsina a 2018.

Ta fara karatun frimare ne Aya Primary School Funtua inda ta samu shaidan kammala karatun frimare a 1980.

Daga nan ta tafi FGGC Bakori a Katsina daga 1981 zuwa 1985. A 1985 ta fara karatun lauya a Kwallejin koyan aikin lauya da karatun addinin musulunci na jihar Katsina da yanzu ya zama Usman Katsina State Polytechnik inda ta samu diploma a karatun lauya a 1987.

Safiya Badamasi ta fara aiki ne a Ma'aikatan Kasuwanci da Yawon Bude Ido na Katsina daga 1989 zuwa 1990.

Daga baya ta koma Ma'aikatar Shari'a na jihar Katsina inda ta fara aiki a matsayin jami'ar shari'a har ta kai matsayinta na Shugaban hukumar/Famanen Sakatare.

Kawo yanzu, ta yanke hukunci a kotun koli da kotunan daukaka kara da manyan kotu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel