Turawa keyi ma Najeriya bakincin samun wutar lantarki

Turawa keyi ma Najeriya bakincin samun wutar lantarki

Ministar kudin Najeriya Kemi Adeosun ta yi zargin cewa kasashen yammacin duniya ne ke yima Najeriya bakin ciki a yunkurin da kasar ke yi na samun hasken wutar lantarki ta hanyar makamashin kwal.

Ministar ta yi wannan zargi ne a Amurka, inda ake yin taro tsakanin kasashen da suka ci gaba da bankin duniya da kuma asusun ba da lamuni na duniya kan yadda za a cike gibin da aka samu na abubuwan more rayuwa.

A cewarta wanda muna son gina tasoshin samar da hasken wutar lantarki ta amfani da kwal saboda Allah ya albarkaci kasarmu da ma'adinin, amma kasashen yammacin duniya na yi mana tarnaki kan shirinmu saboda suna ganin yin amfani da kwal zai gurbata muhalli. Gaskiya ba a yi mana adalci ba.

Ministar ta Najeriya ta kara da cewa kasashen yammacin duniyar sun umarci Najeriya da ta yi amfani da hasken rana da sauran hanyoyin da ba sa yin illa ga muhalli idan tana son samar da hasken wutar lantarki.

Kemi Adeosun ta ce an gina duk wasu abubuwan ci gaban kasashen yamma ne ta hanyar amfani da makamashin kwal, don haka bai dace a hana kasashe irinsu Najeriya yin amfani da shi domin ci gaban kasashensu ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel