Buhari zai amsa gayyatan majalisa amma da sharadi 1

Buhari zai amsa gayyatan majalisa amma da sharadi 1

- Shugaba Buhari yace zai amsa gayyatan majalisar dokokin najeriya idan sun biyo hanya madaidaciya wajen gayyatar sa

- Game da cewan Garba Shehu, akwai hanyar tattaunawa tsakanin fadar shugaban kasa da majalisan dokoki wanda ba’ayi amfani da shi ba

Buhari zai amsa gayyatan majalisa amma da sharadi 1

Fadar shugaban kasa ta bada sharadi 1 akan amsa gayyatar Shugaba Buhari majalisan dokokin tarraya.

Amma, mai Magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu yace har yanzu ba’a i kafar da yakamamta abi wajen gayyatar shugaban kasa ba.

Yayinda yake magana da Jaridar Vanguard, Shehu yace akwai hanyoyin da fadar Shugaban kasa da majalisa ke ganawa, kana dole sai an bi wadannan hanyoyi kafin Buhari ya amsa gayyatar su.

KU KARANTA:Sojoji sun hallaka dan kunar bakin wake a Maiduguri

Yace: “Akwai kafar tattaunawa tsakanin shugaban kasa da yan majalisa. Idan sukayi amfani da wannan kafa,shugaban kasa zai bada martani. Amma a yanzu, kawai labarin jaridu ne kuma ba gayyata ba, idan sukayi gayyata, shugaba Buhari zai amsa.

Kafin yanzu, majalisan dokokin tarayya ta gayyaci shugaban kasa da ya zo yayi fashin baki  akan abubuwan da yakeyi domin magance tabarbarewan tattalin arzikin kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel