Sheikh Dahiru ya gargadi Sanatocin Najeriya

Sheikh Dahiru ya gargadi Sanatocin Najeriya

Babban Shehin Malami Sheikh Dahiru Bauchi ya ja kunnen Sanatocin Najeriya

Sheikh Dahiru Bauchi ya gargadi Sanatoci game da yunkurin raba kason gadon maza daidai da mata

Babban Shehi Dahiru Bauchi yace wannan ya sabawa addini

Sheikh Dahiru ya gargadi Sanatocin Najeriya

 

 

 

 

Babban Shehin Malamin nan na Musulunci Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya gargadi Sanatocin Najeriya game da yunkurin kawo wata doka da za ta sa rabon gadon namiji ya zama daidai da na diya mace a Kasar nan.

Babban malamin addinin yayi wannan jan-kunnen ne a gidan sa yayin da yake ganawa da manema labarai. Sheikh Dahiru Usman Bauchi yace irin wannan kudiri ya sabawa addinin musulunci gaba daya. Babban Shehin Malamin ya gargadi Sanatocin da su guji kawo irin wannan doka Majalisa.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya aika da kasafin kudin badi

Babban Shehin Malami Sheikh Dahiru Bauchi yayi kira ga Sanatocin Kasar da su bi a sannu game da abubuwan da suka shafi addini a Kasar. Sheikh Dahiru Bauchi yace musulunci ya tsara ka’idar rabon gado a Kur’ani.

Sheikh Dahiru Bauchi ya gargadi Sanatoci da su gujewa irin wannan yunkuri, Shehin yace duk wanda ya sanya hannu a irin wannan doka, to yayi wa kan sa. A musulunci dai namiji yana karbar biyun abin da mace ke karba. Sai dai Sanatocin Kasar suna nema a daidaita kason namiji da mace a Kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel