Shugaba Buhari zai bada kyautar jiragen sa

Shugaba Buhari zai bada kyautar jiragen sa

Fadar shugaban Najeriya ta ce shugaban kasar Muhammadu Buhari zai mika wasu karin jiragen samansa ga rundunar sojin sama ta kasar baya ga biyun da aka saka a kasuwa.

Shugaba Buhari zai bada kyautar jiragen sa
Buhari ya yabi shugabannin masana'antu kan gudunmawar su ga tattalin arziki

Da yake zantawa da majiyar mu a babban birnin kasar Abuja babban mataimaki na musamman ga shugaban kan watsa labarai Malam Garba Shehu, ya ce daga cikin jiragen shugaban kasa akwai wadanda ake ganin za su amfani rundunar sojojin sama kuma za a aika ma ta da su.

Ana sa ra nan da 'yan kwanakkin da ke tafe kwamandan da ke kula da jiragen fadar shugaban kasa zai hadu da babban hafsan sojojin sama domin mika masa wadannan jiragen, in ji shi.

Rage yawan jiragen da shugaban kasar ke amfani da su dai na daga cikin alkawurran da shugaba Buhari ya yi kafin hawansa mulki a bara domin yin tsimin kudin da ake kashewa wajen kula da su.

Amma kuma shugaban ya ci gaba da amfani da garken jirage saman guda 10 da ya gada daga tsohon shugaba Goodluck Jonathan fiye da tsawon shekara daya; sai ranar Talata lokacin da aka sanar da matakin na sayar da biyu daga cikinsu.

A kwanan baya ne dai gwamnatin Nageriya ta tallata jirage biyu dake cikin rukunin jirage goma na fadar shugaban kasa.

Gwamnatin tayi bayani dalla-dalla a wata sanarwa da aka buga a wasu jaridun kasar kan yanayin jiragen da hotunan ciki da wajensu da kuma ingancinsu.

Sanarwar ta ce ana so a siyar da jiragen biyu kirar Falcon 7X da kuma Hwker 4000 da zarar an samu mai saye.

Kowanne daga cikin jiragen mutune tara yake dauka.

Tun ba yau ba ne 'yan Najeriya da dama suke cewa, kukan karancin kudi da gwamnati ke yi an bar jaki ne ana dukan taiki, saboda yawan jiragen dake fadar shugaban kasa da kuma makuden kudaden da ake kashewa wajen kula da su.

Wadannan jirage dai biyu ne daga cikin goma dake cikin jerin jiragen da ke fadar shugaban Najeriya.

Cikin watan Satumba ne dai mai baiwa shugaban Najeriyar shawara kan yada labarai Malam Garba Shehu ya bayyana ne cewa, gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari tana da shirin rage yawan jiragen dake fadar shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel