Yan bindigan Niger Delta sun sha alwashin yaki da sojoji

Yan bindigan Niger Delta sun sha alwashin yaki da sojoji

- Yan bindigan Niger Delta suna amfani da sallamar shugaban kasa Buhari suna barazanar cewa zasu maganta sojoji

- Kungiyar sun sha alwashin fara yaki da sojoji idan ba’a dakatar da ayyukan sojoji a yankin ba

- Sun zargi sojojin da razana mutane a yankin Niger Delta

Kungiyar yan bindiga mai suna Niger Delta Greenland Justice Mandate (NDGJM) sun yi wani gargadi ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan ayyukan sojoji a yankin Niger Delta.

Kungiyar yan bindigan suyi ikirarin cewa suke da alhakin yawan tahe-tashen bam a bututunan mai da gas sunce bazasu iya zama suna kallon sojoji na cin zarafin mutane a yankin ba.

KU KARANTA KUMA: Fastoci biyu sunyi ma wata duka

Jaridar The Sun ta ruwaito cewa a cikin jawabin da kungiyar ta bayar daga Gen. Aldo Agbalaja wanda ya kasance kakakin kungiyar, ya gargadi gwamnati da ta shirya yaki idan sojoji basu dakata daga ayyukansu ba.

Kungiyar ta kuma sallami barazanar da Shugaban kasa Buhari yayi a sakonsa na ranar bikin yancin kai na cewa zaiyi maganin yan bindiga.

 “A fuskar wani sanannan rashin nasara, sojojin Najeriya na aikata ayyukan da bai dace ba, suna farautar mutane a ko ina, don kawai aka Kaman sun aiki.

 “Yanzu har ta kai sojojin Najeriya na kama mata da sunan yan kungiyar Niger Delta Greenland Justice Mandate, don kawai su rufe kasawar su. Menene alakar mata/matan aure da kungiyar yan bindiga? Sojoji sun fara wuce iyakar su.

KU KARANTA KUMA: Mummunan hatsarin mota ya afku a Jigawa

 “Don haka muna amfani da wannan wasikar don mu gargade ku da ku daina razanar da kuma cin zarafin mutanen mu, idan kuka ci gaba da damun mutanenmu, zaku tursasamu mu fara aiki da shirin da mukayi a baya; sojojinka a dukan kasar zasu kasance cikin hatsari, zasu zama inda zamu kai harinmu.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel