Tabdijam! Daurin aure cikin ruwa

Tabdijam! Daurin aure cikin ruwa

- Tabbas kowa ya yarda da cewa Soyayya gamon jinni ce, amma idan da kauna

- Akwai wani alaka da shauki na musamman tsakanin masoya biyu, ba mai so ya rabu da daya, haka masoya ke ji ma junansu musamman kafin suyi aure.

Sai dai abin haushin shi ne da zarar anyi auren, sai kaga soyayyar dake tsakanin wasu masoyan ta mutu murus! Duk ko da irin soyayyar da aka sha a baya, duk da irin gagarumin bikin da aka yi.

KU KARANTA: Ta kaddamar da kwamitin yima dokokin zaben garambawul

Sai ga wasu yan kasar Sin sun yanke shawarar daura aurensun yayin da ake tsakiyar saukar da ruwan sama, duk da karfin damina da ake yi. Masoyan sun nuna cewa karfin ruwan sama ba zai iya hanasu tabbatar da soyayyar su ga juna ba.

Masoyan sun shiga cikin wata karamar kwalekwale inda suka zagaya a cikin ruwan, masoyan yan kasar Sin basu damu da ruwan saman ba, damuwarsu kawai shi ne su tabbatar ma juna da tsananin soyayyarsu a ranar bikin nasu.

Ga wasu hotunan su.

Tabdijam! Daurin aure cikin ruwa
Tabdijam! Daurin aure cikin ruwa
Tabdijam! Daurin aure cikin ruwa

Asali: Legit.ng

Online view pixel