Kamfanin sirikin Buhari ya cinye kudin yan gudun hijira

Kamfanin sirikin Buhari ya cinye kudin yan gudun hijira

Legit.ng ta samu labarin cewa daya daga cikin kamfanin da ake zargi da karkatar da kudaden tallafa ma yan gudun hijira, mallakin wani sirikin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne.

Alhaji Mamman wanda da yake a wurin Buhari, shi ne uban matar mai kamfanin.

Majiyar mu ta gano mana cewa Alhaji Bachir Sunusi Dantata da babansa Bachir Dantata ne masu kamfanin, amma Legit.ng ba zata iya tabbatar da ikirarin mallakin ba, sai dai wannan takardar da aka samu daga hukumar yima kamfanoni rajista (CAC) na nuni da cewa akwai kamshin gaskiya a zargin.

Kamfanin sirikin Buhari ya cinye kudin yan gudun hijira

A jiya ne aka ambaci sunan kamfanin a bainar majalisa a matsayin daya daga cikin kamfanunuwa da ake zargin da hannu a cikin badakalar karkatar da kudaden tallafa ma yan gudun hijira. Sanata Bashir Babakaka Gabai daga jihar Borno ne ya fara daga murya kan batun, inda yace duk da makudan kudade da gwamnati ta saki, da kungiyoyi masu zaman kansu, har yanzu babu abin azo a gani a sansanonin yan gudun hijira.

Sanatan yace sama da mutane miliyan 4.5 ne ke tsananin bukatan tallafi, inda sama da mutum miliyan daya ke cikin matsananciyar yunwa. Sanata Gabai yace “a maimakon a kashe ma yan gudun hijira kudaden, sai aka bige da cinye kudaden.”

KU KARANTA: Ta kaddamar da kwamitin yima dokokin zaben garambawul

Ya bada misalin wasu kudade da aka karkatar “an karkatar da kwangilar naira miliyan 80.7 wanda aka ba kamfanin JMT Globat Technologies Ltd don gyaran ofishin yansanda a Kwambir, an karkatar da kwangilan cire shuka masu cutarwa a gaban rafi na naira miliyan 203.357 da aka baiwa kamfanin Josman Technoligies Ltd, sai kuma naira miliyan 117 da aka biya kamfanin Lintex International don samar da matsugunnin wucin gadi, amma kuma bamu ga matsugunnin ba.”

Sai dai shugaban majalisar Sanata Bukola Saraki ya bukaci kwamitin data mika sakamakon bincike da tayi a sati daya, inda ya kara da cewa za’a hukunta duk wanda aka kama da laifi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel