Sabuwa : Shugaba Buhari na cikin ganawa da Oyegun

Sabuwa : Shugaba Buhari na cikin ganawa da Oyegun

- Chief John Odigie-Oyegun ya je Aso Rock Villa domin ganawa da shugaba Buhari

-Har yanzu dai akwai saan kishin8kishin rigimarsu da Tinubu

Sabuwa : Shugaba Buhari na cikin ganawa da Oyegun

A yau ne, Talata, 4 ga watan Oktoba shugaban jam’iyyar APC ta kasa, Chief John Odigie-Oyegun ya kawo ma shugaba Muhammau Buhari ziyara fadar shugaban kasa da ke Aso Villa a Abuja.

Ana sa ran cewa ganawar da suke yi bai wuce akan rigiman da ke faruwa a cikin jam’iyyar tun lokacin da babban jigon jam’iyyar Bola Tinubu ya nemi Chief John Odigie-Oyegunyayi murabus daga matsayinsa na shugaba domin kokarin kunyata jam’iyyar.

KU KARANTA: Obasanjo ya halarci bikin kaddamar da littafin shugaba Buhari

Tinubu ya fiatr da jawabin ne a ranan 25 ga watan satumba ta hanyar mai Magana da yawun sa.

Tsohon gwamnan ya tuhumci Chief John Odigie-Oyegun da laifin cin mutuncin demokradiyya a jihar Ondo yayinda ya aika sunan Rotimi Akeredolu zuwa ofishin hukumar INEC a matsayin zababben dan takara.

Duk da hakan, jigogi biyun sun gaisa jiya a taron kaddamar da littafin tarihin Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel