Obasanjo ya halarci bikin kaddamar da littafin shugaba Buhari

Obasanjo ya halarci bikin kaddamar da littafin shugaba Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da matarsa sun halarci taron kaddamar da littafin shugaban, mai suna ‘Buhari: The Challenge of Leadership’ a dakin taro na kasa da kasa dake Abuja, 3 ga watan Oktoba.

Obasanjo ya halarci bikin kaddamar da littafin shugaba Buhari
Shugaba Buhari tare da Farfesa Paden

Shugaban kasar Bini Patrice Talon, na Chadi Idriss Deby da na Nijar Muhammadou Issoufou sun halarci taron kaddamar da littafin. Hakazalika babban bako a taron shine tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo.shima tsohon shugaba Yakubu Gowon ma na daga cikin manyan baki da suka samu halartan bikin.

Obasanjo ya halarci bikin kaddamar da littafin shugaba Buhari
shuwagabnnin kasashen Bini, Chadi da Nijar

KU KARANTA: An sake gano dala miliyan 40 a asusun Patience Jonathan

Shugaban kasa Buhari ya yabawa marubucin littafin Farfesa JN Paden saboda kokarin da yayi wajen tattara littafin. Farfesa Paden marubuci dan kasar Amurka, kuma kwararrre ne a harkar ilimin kasa da kasa wanda yana da ilimin Najeriya sosai da sosai.

Obasanjo ya halarci bikin kaddamar da littafin shugaba Buhari

Bugu da kari Farfesa Paden shi ya rubuta fitaccen littafin tarihin Ahmadu Bello Sardauna, tsohon Firimiyan yankin Arewa mai suna “Values and Leadership in Nigeria” a shekarar 1986.

Asali: Legit.ng

Online view pixel