Tinubu ya hadu da Oyegun a Abuja

Tinubu ya hadu da Oyegun a Abuja

- Kwanaki kadan bayan hayaniyar tinubu da oyegun, sun hadu a Abuja

- Mambar kwamitin aikin jam'iyyar, mallam Ismaila Isa ya kalli yadda Tinubu da Oyegun ke gaisawa a taron

- Sun hadu a taron kaddamar da littafin tarihin Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Tinubu ya hadu da Oyegun a Abuja
Buhari Tinubu, Oyegun

Game da cewar Jaridar Vanguard, jigogin biyu sin gana ne a taron kaddamar da littafi da ke magana akan tarihin shugaba buhari mai suna 'Muhammadu Buhari: kalubalen shugabanci a Najeriya. Wanda akayi a ICC a Abuja.

KU KARANTA: Labari da dumu-duminsa: An sace tsohuwar Ministan Jonathan a Kaduna

Zaku tuna cewa babban jigon APC, Bola Ahmed Tinubu ya nemi Shugaban Jam’iyyar APC, John Oyegun yayi murabus saboda neman bata sunan jam’iyya. John Oyegun ya kai sunan Rotimi Akeredolu ofishin hukumar INEC a matsayin dan takaran jam’iyyar bayan an bada rahoton cewa an samu magudi a zaben fidda gwanin da aka gudanar.

Shi kuma oyegun a wajen mayar da martanin sa, yace ba zai fadi komai ba akan wannan batu sai ya hadu da Tinubu da kansa . toh gashi Allah ya hada su.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel