Soji sun bayyana wani sirrin su a kan yan matan Chibok

Soji sun bayyana wani sirrin su a kan yan matan Chibok

Rundunar sojin saman Najeriya, ta ce irin girman da kasurgumin dajin nan na Sambisa yake da shi ne, ya sa jiragen su ba sa iya yin shawagi a ko'ina.

Babban Hafsan rundunar, Air Marshal Sadik Baba Abubakar, a wata hira ta musamman da ya yi da majiyar mu, ya ce girman dajin ya kai girman murabba'i dubu 60.

Hakan ne ya sa ba zai yiwu ba ace jiragen da rundunar take da su, su iya karade duk wani lungu da sako na dajin.

Sai dai kuma Air Marshall Sadiq, ya ce daga farkon shekarar nan zuwa yanzu, rundunar ta yi shawagi a kan dajin fiye da na awani 1,260.

Ya kara da cewa duk da cewa har yanzu ba su samu damar ceto 'yan matan na Chibok ba da ma sauran 'yan Najeriya, rundunar ba ta bari 'yan Boko Haram din su fita daga dajin domin zuwa su sake yin garkuwa da wasu.

Dangane kuma da ikrarin da Boko Haram ta yi a kwanakin baya, a wani faifan bidiyo cewa wasu daga cikin 'yan matan na Chibok sun mutu, a hare-haren da rundunar ta kai dajin, Babban Hafsan ya ce farfaganda kawai irin ta 'yan ta'adda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel