Wani mutum farin fata ya karya dokar hanya a Abuja

Wani mutum farin fata ya karya dokar hanya a Abuja

Wani dan kasar waje yayi karya dokar hanya kuma yayi raini ga Shugaban kasa Muhammad Buhari.

Kamar yadda wani mai amfani da dandalin sadarwa na Facebook mai suna Emmanuel Ogbeche, ya saka wani abun mamaki a shafin sa na Facebook, yace farin fata yaso ya janyo hatsari a mahadar power house, Asokoro Abuja jiya 3 ga watan Oktoba, amma lokacin da ma'aikatan hanya suka yi mai magana, sa ya kawo raini ga Buhari.

Wani mutum farin fata ya karya dokar hanya a Abuja

Karanta abunda ya rubuta:

Wannan wawan , eh sakarai ne, ya kusan yasa ayi hatsari a kan mahadar power house Asokoro Abuja, yan mintunan da suka wuce.

Lokacin da ma'akatan hanya suka zo dan suyi mai magana, har yana da bakin da ze iya budewa yace wai ba abunda ze faru ko da Buhari na gurin. Mu cigaba da saka wannan abun da ya faru da musa gwamnati ta ki amincewa da zaman shi a kasar mu.

Wani mutum farin fata ya karya dokar hanya a Abuja

Daga ganin lambar motar, kasan yana cikin wakilan kasar waje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel