Makarantan NAIJ.com sun goyi bayan Rahama

Makarantan NAIJ.com sun goyi bayan Rahama

- Labaran fittacciyar jaruma Rahama Sadau da aka kora daga wasa ya samu halayya daban-daban

- Makarantan shafin Legit.ng sun nuna ra’ayinsu game da dukkan al’amarin

- Kaso 12 cikin 100 sun amince a koreta yayinda kaso 53 cikin 100 suke gannin korarta a matsayin shirme inda kaso 35 cikin 100 suka nuna rashin damuwa game da dukkan al’amarin

Makarantan Legit.ng sun goyi bayan Rahama
Jaruma Rahama Sadau

Kungiyar Motion Pictures Practitioners Associaton of Nigeria (MOPPAN) sun kori fittacciyar jarumar Kannywood da Nollywood  Rahama Sadau a ranar Lahadi, 2 ga watan Oktoba na shekara 2016, saboda yanayin da ta fito a wani biyon mawaki ClassiQ.

Makarantan Legit.ng sun goyi bayan Rahama
ClassiQ

A halin aynzu, ClassiQ ya fito ya bayyana cewa baiji dadin hukunci da korar da Rahama ta samu ba. Ya bayyana wa jaridar Premium Times cewa “Ni na bukaci kuma na roki Rahama Sadau da ta fito a bidiyo na saboda ita fittacciya ce a masana’antun nishadi shikenan ba wai don wani abu ba. Na sa tane saboda ina son fittaccen fuska a bidiyon,” cewar sa.

KU KARANTA KUMA: Yarinyar da ta haihu tun tana Firamari

 “Lokacin da abubuwa suka juye a kanta kan yadda ta fito a bidiyon, ya zo mun a bazata. Har yanzu na kasa dawowa daidai. Nayi juyayi kan Koran nata. Har yanzu ina jin wannan yanayi a ce an koreta daga masana’anta saboda ta fito a bidiyona ba abune mai kyau ba ko kadan. Mutun ce mai kirki, ya kara.”

Wannan korar nata da akayi ya samu furuci daban-daban daga mutane. Yayinda wasu yan kungiyar MOPPAN suke ganin korar nata shine dai-dai, wasu suna ganin hakan baida fa’ida. Haka kuma wasu basu damu da al’amarin dukka ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel