Buhari ya samu yabo daga shugabanni

Buhari ya samu yabo daga shugabanni

- Tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon (mai ritaya) ya yabi shugaban kasa sosai a jiya Litinin 3 ga watan Oktoba

- Gowon ya bayyana Buhari a matsayin mutun mai yaki don ingantancen shugabanci

- Ya kuma bayyana cewa Buhari ya shiga Aso Rock a zaben da akayi kamar mai yaki

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu lambar yabo daga mashawarta a gurin kaddamar da litattafinsa mai taken Muhammadu Buhari: kalubalan shugabanci a Najeriya.

Buhari ya samu yabo daga shugabanni
Shugaban kasa Buhari na musabaha da mawallafin littafin; Farfesa John Paden yayinda tsofaffin shugabannin kasa, Yakubu Gowon da Olusegun Obasanjo ke kefensa

Farfesa John Paden, wa wani marubucin Amurka tare da ra’ayi na musamman a ci gaban Najeriya, jaridar Guardian ta ruwaito.

A taron, tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon da Olusegun Obasanjo sun girmama nagartan Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda suka bayyana a matsayin yaki don ci gaban shugabanci na gari.

KU KARANTA KUMA: Yarinyar da ta haihu tun tana Firamari

Buhari ya samu yabo daga shugabanni
Shugaba Buhari tare da shugabannin kasar Chadi da jumhuriyar Niger sun hallarci taron

Gowon, wadda ya kasance Ciyaman na taron ya fada ma mahalarta taron cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cancanci yabo da zargi daga yan Najeriya.

Ya kuma bayyana shugaban kasa a matsayin mayaki kuma mutumin dake da burin ganin komai ya daidaita ta fannin tattalin arziki duk da babban kalubale da kasar ke fuskanta.

Buhari ya samu yabo daga shugabanni
Shugaba Buhari, matar sa Hajiya Aisha Buhari, Janar Yakubu Gowon da Olusegun Obasanjo da kuma sauran shugabannin kasashen waje

A bangarensa, Obasanjo ya ce takardan ya tabbatar da Buhari a matsayin mai gaskiyar da ya ke kamar yadda ya san shi. Ya bayyana cewa ya zama lallai wadanda keda ra’ayin tsinkayo cikakken yadda Najeriya take a jiya da kuma yadda shugabannin ta suke tuka al’amuran kasar a yau.

Ya ce ko da yake takardan ta tabbatar da abunda ya sani game da Buhari, bai tabbatar da kima na shugaban kasa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel