Mutum takwas sun rasa rayukansu a hatsarin mota

Mutum takwas sun rasa rayukansu a hatsarin mota

A kalla mutane 8 ne suka rayukansu a yayin wani hastarin mota a kan hanyar Hadejia zuwa Kano a karamar hukumar Kaugama na jihar Jigawa.

Mutum takwas sun rasa rayukansu a hatsarin mota

 

Mai magana da yawun hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) na jihar Adamu Abdullahi ya bayyana cewa hatsarin ya faru ne da yammacin ranar Lahadi 2 ga watan Oktoba.

Abdullahi yace: “Jami’an mu na kan hanyar dawowa ne daga Hadejia lokacin da suka tsinci hatsarin, daga nan ne suka tsaya don ceton masu rai a cikinsu, inda suka mika gawawwakin mamatan zuwa asibiti mafi kusa.”

KARANTA:Sojan Najeriya ya taimaka wajen karbar haihuwar wata mata

Wani majiyar gani da ido Alhaji Salisu Sani yace wata mota kirar Jeep ce tayi arangama da karamar mota kirar Camry.

Shima shugaban hukumar kare haddura ta kasa (FRSC) Angus Ibezim ya tabbatar da faruwar lamarin, yace “mun samu rahoton lamarin, bamu ji dadin hakan ba” daga karshe sai ya gargadi matuka mota dasu daina gudun wuce sa’a a kan hanyoyi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel