Jonathan da mallakar jirgin sama

Jonathan da mallakar jirgin sama

- An ga tsohon shugaba Jonathan da matarsa a wani jirgin sama na alfarma

- Ana rade-radin cewa jirgin mallakin su ne

- Hotunan jirgin ya janyo ka-ce-na-ce

Jonathan da mallakar jirgin sama
Tsohon Shugaba Jonatahn da matarsa da kuma jirgin da ake zargin mallakinsu ne

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan shi da matarsa sun samu kyakkyawar tarba yayin da suka isa filin jirgin saman jihar Rivers a ranar Lahadi 2 ga watan Oktoba a wani karamin jirgin sama na alfarma mai daukar mutane kalilan.

Jonathan da mallakar jirgin sama
Jonatahn da 'yan tarbensa a filin jirgin na Rivers

Wani mai suna Amos Akere wanda ya yada hotunan tsohon shugaban da matar tasa a lokacin da suke sauka daga cikin jirgin yana mai cewa, “Ga baban dimukuradiyya da matarsa Patience a garin Fatakwal…”

Wadannan da sauran kalamai na yabo da ya lika a shafinsa a dandalin sada zumunta da muharawa sun janyo ka-ce-na-ce, domin yayin da wasu ke yabon tsohon shugaban, wasu kuma na sukar sa da kuma zargin cewa shi ya jefa kasar nan a halin tattalin arzikin da ta ke ciki.

Jonathan da mallakar jirgin sama
Sabuwar shigar matar tsohon shugaban da 'yan jarida ke cewa ko a jikinta, dangane da rigimar da ke tsakaninta da Hukumar EFCC dangane da wasu miliyoyin daloli a banki

Daya daga cikin masu wannan ra’ayi shi ne wani mai suna Murtala Sani, wanda ya ke cewa, a marataninsa dangane da nagartar shugabancin na Jonathan da kuma matarsa Dame Patience, “tun da labarin badalar kudade  dangane da matar Jonathan ta bazu, al’ummar duniya na tambayar ta yaya za a ce mutum daya ya bude asusun ajiyar banki guda biyar, a kuma ranar daya? Ba mamaki matar ta dage a yakin neman zaben mijinta har kuma ta ke kiran Buhari mai matacciyar kwakwalwa, gaskita dai yanzu ta yi halinta.”

Wata kuma mai suna Chijioke Micheal Igbokwe na cewa: “Gwani na gwanaye, shugaban da ba a taba kamarsa ba, ba kuma za a sake yin kamarsa ba a Najeriya, ya gina tattalin arziki mai girma a Africa, amma yanzu kuma APC ta karya kasar nan. Yanzu ga shi cin hanci da rashawa yayi yawa a Najeriya sakamakon rashin iya mulki.”

Ana rade-radin jirgin sman da ya dauko tsohon shugaabn da matarsa mallakin su ne, wanda hakan ya dada ingiza janyo martani maras dadi a shafukan sada zumunta da muhawara.     

A kwanan baya dai Hukamar EFCC ta rufe wasu asusun ajiyar banki na matar Jonathan guda biyar da da kimanin Dalar Amurka miliyan 30 a ciki wadanda aka bude da sunayen wasu kamfani.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel