An kori Rahma Sadau sauara Ali Nuhu?

An kori Rahma Sadau sauara Ali Nuhu?

- Jarumar fina-finan Hausa ta janyo ka-ce-na-ce, da kuma an taba dakatar da Jarumar daga fitowa a fina-finai a baya

- A yanzu, shin ko masu shirin fim za su kori Ali Nuhu

Korar da babbar kungiyar masu shirya fina-finan Hausa ta MOPPAN ta yiwa Rahma Sadau daga kungiyar da kuma haramta mata fitowa a cikin fina-finan Hausa ya bar baya da kura.

An kori Rahma Sadau sauara Ali Nuhu?

Yayin da mutane da yawa ke maraba da wannan labari, wasu kuma na ganin an ci da gumin jarumar, kamar yadda jama’a suka cigaba da fadin albarkacin bakinsu a shafukan sada zumunta da muhawara na intanet.

An kori Rahma Sadau sauara Ali Nuhu?
An kori Rahma Sadau sauara Ali Nuhu?

Mabanbantan ra'ayi dangane da matakin MOPPAN kan Rahma Sadau a shafuka sada zumunta da muhawara na Intanet

An kori Rahma Sadau sauara Ali Nuhu?
Nura Hussaini mai fitowa a fina-finan Hausa na daya daga cikin wadanda suka yi kira da a hukunta Rahma Sadau ko su tafi Kotu

A ranar Lahadi 2 ga watan Oktoba ne kungiyar MOPPAN a Kano ta zartar da hukuncin korar Rahma Sadau tare haramta mata sake fitowa a fina-finan Hausa baki dayansa, sakamakon fitowar da jarumar ta yi a wani faifan bidiyo na waka tare da wani mawaki mai suna classiq, a inda ta yi, abin da kungiyar ta ce, abubuwan da suka sabawa dokoki da kuma tsarin kungiyar na da'a.

KU KARANTA KUMA: Dandalin Kannywood: Sadiya Gyale ta yi cikar daki

Cikin sanarwar da kungiyar ta fitar bayan taronta na gaggawa kan batun, ta kuma rarrabawa kafofin yada labarai, ta ce, ta yanke shawarar korarta jarumar ce a matsayin tauna tsakuwa ga duk masu shirin shimfida badala da rashin tarbiyya a fina-finan Hausa.

Har yanzu ba a ji ta bakin Rahma Sadau ba dangane da wannan kora, saboda a cewar wata majiya mai karfi, jarumar ba ta kasar.

Tun bayan sakin faifan bidiyon wakar mai suna Ina kaunar ki da jarumar ta yi da mawakin zamani da aka kira Classiq dan asalin jihar Plato ne, Rahma ta shiga bakin duniya a inda aka yi tir da irin rawar da ta taka.

An kori Rahma Sadau sauara Ali Nuhu?
Wasu na cewa da sauran rina a kaba

A cewar Nura Hussain Jarumi kuma daya daga cikin masu wadanda suka soma kira da a dau mataki kan Rahma Sadau a bisa abin da ta aikata ya ce, ba za su lamunci irin wannan ta’ada ba, domin ko kungiyarsu ba ta dau wani mataki na hukunta Rahama ba, su za su tilasta mata ta hanyar zuwa kotu.

An dai taba dakatar da Rahama Sadau a shekarar 2015 amma bai yi tasiri ba, sai dai yayin da jama’a ke jira su ga tasirin korar, wasu kuma na ganin kungiyar ta daki jaki ne ta bar taiki, domin fitaccen jarumi Ali Nuhu a cewar su, ya aikata abubuwa da suka fi nata muni wasu fina-finai.

Rahama ta shiga uku saboda hakan:

An kori Rahma Sadau sauara Ali Nuhu?
An kori Rahma Sadau sauara Ali Nuhu?
An kori Rahma Sadau sauara Ali Nuhu?

Asali: Legit.ng

Online view pixel