Gamnatin Niger ta rage farashin kaya zuwa rabi

Gamnatin Niger ta rage farashin kaya zuwa rabi

- Gwamnan jihar yace wannan zai kawo saukin sayayya lokacin wanen bukin

- Ya jaddada cewa matsin da jama'a suke ciki ya kai ga masu mulki shi ya jaza haka

- Gwamna Bello yace ba kowa zai amfana da wannan ba

Gamnatin Niger ta rage farashin kaya zuwa rabi
Farashin kayayyakin abinci

Mutanen jihar Neja zasu dara har zuwa karshen shekara yayin da gwamnatin jihar ta fara saida hatsi wadda kudinsu ya kai naira miliyan 183 a farashi mai sauki. Kampanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa ragin zai kawo saukin farashin in aka gwada da na kasuwa.

KU KARANTA: Daga karshe, wanda akebi bashin nan na Abuja ya biya dan siyasar nan bayan da yayi tsirara

Gwamna Sani Bello wanda ya tabbatarda wannan labarin ranar Assabar 1 ga Oktoba yace hawhawar farashin kayayyaki yasa gwamnatinsa daukar wannan matakin. Ya kara da cewa:

"Muna ba abinci da muhalli matukar muhimmanci a rayuwa. Mutane da yawa nada matsalar  sayen abinci tumba lokacin bukukuwa ba. Muna jin matsin da jama'armu ke ciki, shi yasa muka bada karfi wajen saida hatsi a kananan hukumominmu 25 dake akwai a fadin jihar. Saida hatsin a farashi mai sauki na cikin  kokarin gwamnati na tausaya ma jama'a."

Asali: Legit.ng

Online view pixel