Jibrin ya bayyana yadda ake kashe-mu-raba a majalisa

Jibrin ya bayyana yadda ake kashe-mu-raba a majalisa

"Ni Abdulmumini Jibril Kofa na samu naira miliyan dari shida da hamsin na gudanarwa a matsayi na na shugaban kwamitin kasafi.

Jibrin ya bayyana yadda ake kashe-mu-raba a majalisa
Abdulmumin Jibrin

Kakakin mjalisa, Yakubu Dogara ya karbi naira biliyan daya da rabi.

Mataimakin kakakin majalisa, Yusuf Lasun ya karbi naira miliyan dari takwas.

Shugaban masu rinjaye na majalisa Femi Gbajabiamila ya karbi Naira bilyan daya da digi biyu.

Mataimakin Shugaban masu rinjaye na majalisa Buba Jibril ya karbi naira bilyan daya da digo biyu.

Babban Mai Tsawatarwa Na majalisa Alhassan Ado Doguwa shima ya karbi Naira Biliyan daya da digo Biyu (N1.2b)

Mataimakin mai Tsawatarwa ya karbi Naira Miliyan dari Bakwai (N700million)

KU KARANTA KUMA: An kama wasu alkalai da laifin cin hanci da rashawa

Shugaban marasa rinjaye na majalisa Leo Ogar ya karbi naira biliyan daya da digo biyu.

Mataimakin shugaban marasa rinjaye Onyema ya kabi naira milyan dari Takwas.

Mai Tsawatarwa ga marasa rinjaye a majalisa ya karbi naira milyan dari bakwai.

Mai taimakwa mai tsawatarwa na marasa rinjaye shi ma ya karbi naira milyan dari bakwai.

Ina da dukkan shaidun da ake bukata a wajena wadanda za su tabbatar da wannan ikirarin da na yi akan kaina da kuma shugabanin majalisar tarayya karkashin jagorancin Dogara", Inji Honarabul Abdulmumini Jibrin Kofa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel