Al'aurar wata mata na fitar da tsutsa

Al'aurar wata mata na fitar da tsutsa

A wata unguwa mai suna Olakula dake a karamar hukumar Ipokia a jihar Ogun, a samu wata mata mai suna Iya Toheeb wadda ake rade-raden cewa wata cuta ta same ta inda har yasa take fitar da tsutsa daga al'aurar ta.

Majiyar mu dai ta The Nation ta ruwaito cewa jama'ar unguwar sunyi ta tururuwa suna zuwa ganin matar mara lafiya tare da jajantawa iyalanta.

Al'ummar gari kuma dai suna ta rade-raden cewa ko dai tsafi aka yi mata saboda dai dukkan wani magani da aka bata ya ki yayi mata wani tasiri.

KU KARANTA KUMA: EFCC Na Ci Gaba Da Sanya Alamun Tambaya A Kadarorin

Daga baya ne ma dai da yan uwan nata suka ga haka sai suka nemi tsohon mijin ta wanda yake sana'ar kafinta. Da wakilin mu ya tambayi dalilin neman tsohon mijin nata sai daya daga cikin yan uwan ta da ya bukaci a sakaya sunan sa yace: "mun yanke shawarar mu nemo tsohon mijin nata ne don wata kila yana da masaniya ko kuma sa hannu a cikin wannan matsalar tata duba da yadda cutar ta ki ci ta ki cinyewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel