Koma bayan tattalin arziki: Tinubu, Atiku sun kawo mafita

Koma bayan tattalin arziki: Tinubu, Atiku sun kawo mafita

- Bola Tinubu da kuma Atiku Abubakar sun bayar da shawara kan yadda jkasar Najeriya zata iya fita daga koma bayan tattalin arziki

- Tinubu yace koma bayan tattalin arziki na bukatar sadaukarwa daga dukkan yan Najeriya don gannin kasar ta fita daga ciki.

- Atiku a bangarensa yace, kasar ta dogara a kan haraji ba wai mai ba

Asiwaju Bola Tinubu, tsohon gwamnan jihar Lagas kuma shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa baki daya, ya bayyana cewa koma bayan tattalin arziki dake Najeriya, na bukatar sadaukarwa daga dukkan yan Najeriya don gannin kasar ta fita daga mawuyacin hali.

Koma bayan tattalin arziki: Tinubu, Atiku sun kawo mafita
Shugabannin Jam'iyyar APC

Tinubu ya sanar da hakan yayinda yake Magana a cibiyar cininki a lokacin karrama shugabanta, Oluwaseyi Emmanuel Abe, a daren ranar Laraba, 28 ga watan Satumba a jihar Lagas.

A cewar sa, an albarkaci kasar Najeriya da albarkatun mutum da na albarkatun kayayyaki, wanda za’a sarrafasu da kyau don fita daga koma bayan tattalin arziki, jaridar Vanguard ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Shehu Sani ya shawarci Buhari kan kudin Abacha

Har ila yau shugaban jm’iyyar APC ta kasa baki daya yayi Magana kan amfanin wutar lantarki gurin inganta tattalin arziki kamar yadda ya tuna cewa jihar Lagas ta zuba jari a aikin wutar kudi lokacin da yake a matsayin gwamnan jihar.

Da yake Magana a gurin taron, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar yace kasar ta dogara a kan kudin haraji ba wai mai ba.

Atiku ya bayyana cewa babban matsalar Najeriya shine jarabarta a kan kudaden mai dake shiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel