Sarki Sanusi yayi magana kan harin Buhari

Sarki Sanusi yayi magana kan harin Buhari

- Sarkin Kano Lamido Sanusi ya ce rahotanni da akeyi a kan sa na cewa ya kai hari ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, an qirqira ne don a haifar da matsala a tsakaninsa da shugaban kasa

- Sanusi ya bayyana cewa idan ya na so ya kalubalanci gwamnatin a duk gurin da batayi daidai ba, zai bi ta hanyar da ta dace

Sarki Sanusi yayi magana kan harin Buhari
Sarkin Kano Lamido Sanusi yace bai kai ko wani hari ga Buhari

Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi ya karyata rade-raden cewa shi ya taba kai hari ga shuagaban kasa Muhammadu Buhari kan halin da tattalin arziki ke ciki.

Jaridar Premium Times ta rubuta abinda Sanusi yace a wata sanarwa cewa shi bai taba furta furucin da rahotanni ke cewa ya kai hari ga Buhari ba.

KU KARANTA KUMA: Zaben jihar Edo: Ku duba sakamakon zabe daga hukuma

Ya bayyana cewa “kage akeyi mun don a haifar da rashin jituwa da matsala a tsakani na da shugaban kasa”.

Ya kara da cewa: “An jawo hankalina ga wasu maganganu da aka ce na kai hari ga gwamnatin Janar Buhari da jam’iyyarsa na kuma yabi jam;iyyar adawa, ban san wanda ke makarkashiya kan wadannan zancen ba.

Sarki Sanusi yayi magana kan harin Buhari
Sanusi Lamido Sanusi tare da Archbishop of Canterbury

“Amma da alama wannan na daga cikin sabon tsari inda ake alakanta maganganu ga mutane don mutun ya samu matsayi a siayasa ko kuma ya shuka rashin jituwa a tsakanin mutane.

 “Rahotanni da ake Magana a kai bai bayyana a gurin da nayi jawabina da kuma a gaban wanda da nayi, haka kuma matsoratan da suka shirya makarkashiyar basu samu karfin gwiwar da zasu rubuta sunayen su ba."

KU KARANTA KUMA: Oshiomhole yayi nasara a mazabar sa

Sanusi yace: “Abune da kowa ya kani cewa an saukar dani daga kan matsayina na gwamnan babban bankin kasa saboda aikina na tona asirin yawan  satar kudin kasar mu daga gwamatin da, da kuma cewa na nuna goyan bayana dari bisa dari kan yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin yanzu kenan.

Ya kammala da cewa a lokacin da yaso ya bayar da suka ga gwamnati, zaiyi ne a bude a kuma cikin hanyar da ta dace amma ba wai ta hanyar kalaman keta a kafofin watsa labarai ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel