Kungiyar kare hakkin bil'adama ta zargi gwamnatin Najeriya

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta zargi gwamnatin Najeriya

A cewar rahoton da Kungiyar kare hakkin bil'adama (Amnesty International) ta fitar a ranar ta Laraba ta na da bayanai na jami'an tsaro sun tsare masu fafutikar Biafra, wasu sun bace baya ga wadanda suka rasu a hannun jami'an tsaro a Najeriya.

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta bayyana cewa Najeriya na kokari da barazana ta rufe baki da ma yin barazana ga 'yan jarida da masu zanga-zanga.

A cewar kungiyar wacce ke da ofishinta a birnin London cikin zanga-zangar da ta bayyana a baya-bayan nan akwai hana masu fafutika daga kungiyar nan mai kokari na ganin ansako 'yan matan Chibok sama da 200 da ke hannun Boko Haram, da hana 'yan Shi'a zanga-zangar a sako malaminsu bayan tsawon lokaci ya na hannun mahukunta da masu fafutikar samun 'yancin yankin Biafra a Kudu maso gabashin na Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel