Sunan Abdulmutallab ya fito cikin rajistar masu zabe ta Edo

Sunan Abdulmutallab ya fito cikin rajistar masu zabe ta Edo

- Hoton Umar Farouk Abdulmutallab ya fito cikin ranistar masu zaben Edo

- Wannan abin takaici ne domin Abdulmutallab yana jarun a Amurka inda aka bashi daurin rai-da-rai dalilin ta'addanci

- Gwamna Oshiomhole ya koka game da sahihancin zaben gwamnan

Sunan Abdulmutallab ya fito cikin rajistar masu zabe ta Edo
Adams Oshiomole

Umar Farkouk Abdulmutallab wanda aka daure kan laifin ta'addanci a Amurka ya fito a cikin rajistar masu zaben gwamnan jihar Edo. Abdulmutallab wanda aka yankema hukuncin daurin rai-da-rai domin kokarin tayar da bam, amma abin mamaki sai ga hotonsa a cikin rajistar karya, inji  gwamna Adams Oshiomhole.

KU KARANTA: Bangarorin Jam’iyyar PDP sunyi ganawar sulhu

NAN ta ruwaito gwamnan na wannan koken lokacin da wani ma'aikacin ofishin jakadancin Amurka  Mista F John Bray  ya ziyarce shi a Lagos. Gwamnan Edo yace, duk da yake hoton dan ta'addar na dauke da suna irin na 'yan Benin zai iya sa shakku kan sahihancin zaben da za'a yi kusan tsakanin 'Yan takarar All Progressive Congress Godwin Obaseki da pasto Ize Iyamu na Peoples Democratic Party (PDP).

Asali: Legit.ng

Online view pixel