Yan Boko Haram sun afka ma wata kauye kusa da Chibok

Yan Boko Haram sun afka ma wata kauye kusa da Chibok

Wasu yan bindiga dadi da ake kyakkyawan zaton yan kungiyan boko haram ne sun kai hari kauyen Kuburvwa, a jihar Borno.

Yan Boko Haram sun afka ma wata kauye kusa da Chibok
Boko Haram

Yan bindigan sun kai harin misalign karfe 6:30 na yamma suna harbin kan mai uwa da wabi, wanda ya sanya mazauna suka arce cikin daji domin cecen rayukansu.

Wani ma’aikacin yan banga,Mr Gava, ne ya bayyana haka a wata waya da yayi ga wani dan jaridan Premium Times daga Maiduguri.

KU KARANTA: Abubuwa 6 da Nnamdi Kanu ya fadawa masoyansa a Kotu

Yayinda yake bayani yace : “ Yanzun nan da nike muku Magana, yan bindiga na banka ma gidaje wuta suna Koran mazauna kauyen. Bisa ga labarin da muka samu daga jami’an mu a Chibok da Kautikari, ba zamu iya fadin rayuka nawa aka rasa ba yanzu saboda har yanzu yan boko haram din na kauyen.

Zaku tuna cewa wannan kauyen ne yan Boko Haram suka kai hari ranan 21 ga watan Agusta inda suka kasha akalla mutane 11 kuma suka yi ma mata fyade.

Asali: Legit.ng

Online view pixel