Mawuyaci ne mutane su yarda da girman wannan machijiyar

Mawuyaci ne mutane su yarda da girman wannan machijiyar

Shin wai wani irin girma ne Machijiya take iya kaiwa? Zaka Iya kasancewa cikin tunani da zullumi kuma baka iyayin gardama. Haka kuma zakaji dadi idan baka hadu da irin wannan abun tsoron a cikin daji ba.

Mutane suna Sharan babban wani fili, inda suke cire itatuwa da chiyayin dake cikin filin. Sai kawai suka gamu da wannan katuwar machijiyar, inda mutanen sukaji tsoron kusantar wajen.                Amman daga baya, yadda suka fitar da machijiyar daga cikin filin abun mamaki ne. Duk da cewar sun kasa daukar machijiyar saboda girman ta.

Mawuyaci ne mutane su yarda da girman wannan machijiyar

Inda sukayi sa'a suna da motocin gini a cikin filin a lokacin. Sai sukayi amfani da guda daya suka fitar da machijiyar daga cikin wajen. Wannan abun ya zama abin mamaki sosai.

Amman daukota a abin hawa shine wani abun matsala kuma, saboda basuso su kashe wannan babbar hallitar mai ban mamaki. Saboda haka, sai sukayi amfani da wani katon abu mai fadi tare da katuwar kacha, inda sukayi amfani da abubuwan domin su taimaka wajen rike machijiyar a lokacin da ake tafiya da ita a mota.

Wani mutum dake wajen, yaji dadin al'amarin, inda yayi ta kaiwa yana komowa yana daukar machijiyar a wayar hannun sa, daga kanta zuwa bindin ta.

Wannan katuwar machijiyar tanada matukar ban mamaki. Sabod haka ya kamata mutane su dungayin hankali da irin wadannan kattin machizain alokacin da suke cire itace da ciyayi a filayen su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel