Bikin cika shekara guda na jikanyar Goodluck Jonathan

Bikin cika shekara guda na jikanyar Goodluck Jonathan

Jikanyar tsohon shugaba Goodluck Jonathan Princess Eliana Godswill-Edward ta cika shekara guda a ranar 22 ga watan satumba.

Bikin cika shekara guda na jikanyar Goodluck Jonathan

Iyayen masu suna Faith da Edward, sun shiya mata gagarimar biki a ranar data cika shekara gudan.

Idan dai za'a iya tunawa, ma'auratan Elizabeth Faith Sakwe diyar tsohon shugaba Goodluck Jonathan, ta auri abokin rayuwar tane mai suna Godswill Osim Edward a ranar 5 ga watan Afirilun shekarar 2014 a Bayelsa, sannan kuma ranar 12 ga watan Afirilun shekarar ta 2014 aka kara gudanar da biki a garin Abuja.

Bikin cika shekara guda na jikanyar Goodluck Jonathan
Bikin cika shekara guda na jikanyar Goodluck Jonathan

Tsohon shugaba Goodluck Jonathan yana da yara wa'anda yake rukon su, wa'anda bashi ya haifesu ba, a inda Faith Osakwa na daya daga cikin su. Majiya ta tabbatar mana da yarda shugaban da matarsa Patience Jonathan suka rike Faith da sauran yan uwanta da suke iyaye daya dasu tun a shekarar 2000.

Acewar rahoton, Faith yarinyar Engr. Ukaliziba Sakwe ce, wato babban jigo a jam'iyar PDP na jahar Bayelsa, sannan kuma babban aminine a wajen Jonathan.   Wanda yayi hatsarin mota ya mutu a shekarar 2000.

Bayan mutuwar nasa ne, tsohon shugaban da matarsa suka dauki yaran nasa guda hudu, Faith, Arewere Adolphus, Aruebai da kuma Abeyola, inda suka dauki nauyin cinsu da shansu da suturansu da kuma karatunsu tun bayan shekaru 14 kenan.

Bikin cika shekara guda na jikanyar Goodluck Jonathan

Barka da zagayowar ranar haihuwar Gimbiya Eliana Godwill-Edward!

Asali: Legit.ng

Online view pixel