Taron UN: Nasarorin da Najeriya ta samu-Shugaba Buhari

Taron UN: Nasarorin da Najeriya ta samu-Shugaba Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana wanda kasar Najeriya ta samu nasarorin a taron majalisar dinkin duniya. 

Taron UN: Nasarorin da Najeriya ta samu-Shugaba Buhari

 

 

 

 

Shugaba Muhammadu Buhari zai dawo Najeriya ranar Lahadin yau daga Taron Majalisar dinkin duniya da aka yi a Kasar Amurka. Shugaban Kasar ya bayyana cewa an dace kwarai a wannan tafiya da yayi zuwa Amurka. Yayin da yake ganawa da ‘yan jaridu Birnin New York na Kasar, Shugaba Buhari ya bayyana irin nasarorin da aka samu a tafiyar.

Femi Adesina ya fitar da jawabi game da alfanun wannan tafiya zuwa New York. Mai magana da bakin Shugaban Kasar ya dai bayyana cewa Muhammadu Buhari ya fadawa sauran Shugabannin Kasashen duniya cewa dole fa su tashi tsaye wajen taimakon juna da fada da talauci, da kuma sauyin yanayi da ta’addanci idan har ana nema duniyar nan tayi kyau. Shugaba Buhari ya kuma yi magana game da ‘yan gudun hijirar Najeriya; wanda rikicin Boko Haram ya afka da su, Shugaban Kasan yayi kira da cewa ya zama dole a maida wadannan mutanen gidajen su.

Shugaban Kasar ya kuma bayyana cewa Najeriya ta ci karo da matsalar tattalin arziki saboda abin da ya shafi harkar mai a duniya. Shugaba Buhari yace Kasar ta fara komawa harkar gona da kuma ma’adanai da sauran su domin shawo kan wannan matsalar. Har wa yau Najeriya ta fada kokarin gina abubuwan more rayuwa domin cigabar Kasar da ‘ya ‘yan ta. Kasar Najeriya za tayi kokari wajen kawo ‘yan kasuwa daga kasashen duniya su zuba jari a Kasar.

KU KARANTA: UN: Shugaba Buhari ya tafka hannu a wata muhimmiyar yarjejeniya

Shugaba Buhari ya kuma kara jadadda aniyar sa, na fada da sata a Kasar, ya kuma bayyana cewa yakin da suke yin a cin hanci yana bada sakamako, yanzu haka, an fara samun abin da ba za a rasa ba. Shugaban Kasar yayi jawabi game da sauyin yanayi a Yankin Kasahen. Shugaba Buhari ya kuma nuna goyon bayan Kasar Palestine.

Shugaban Kasar dai ya gana da Shugabannin duniya da manyan ‘yan kasuwan Amurka domin cigaban Kasar. Ana sa rai Shugaba Buhari ya dawo Najeriya a yau dinnan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel