Agbakoba ya hankaltar da Buhari kan siyar da dukiyoyin kasa

Agbakoba ya hankaltar da Buhari kan siyar da dukiyoyin kasa

- Tsohon shugaban kungiyar Nigerian Bar Association (NBA), Dr. Olisa Agbakoba yace Shugaban kasa Buhari na bukatar yin abubuwa guda biyu kafin ya siyar da wasu dukiyoyin kasa.

- Ya bada shawaran cewa gwamnati na daukan wani kaya na kudi da kuma kayan da ake bukata kafin tayi zancen siyar da dukiyar

Agbakoba ya hankaltar da Buhari kan siyar da dukiyoyin kasa
Agbakoba ya shawarci shugaba Buhari da yayi koyi da tsarin shugaba Obama kan koma bayan tattalin arzikin Amurka

Tsohon shugaban kungiyar Nigerian Bar Association (NBA) Dr. Olisa Agbakoba ya hankaltar da shugaban kasa Muhammadu Buhari kan gaggawan siyar da wasu dukiyoyin kasar.

KU KARANTA KUMA: Yan Najeriya na harin gwamnatin Buhari kan bashi

Da yake jawabi a kan kiran da akayi kwanan nan daga wasu fitattun yan Najeriya wanda suka bayar da shawarwari game da sayar da dukiyar kasa a matsayin hanyar farfado da tattalin arzikin kasar, Agbakoba yace Buhari na bukatar yin abubuwa guda biyu kafin ya siyar da wasu dukiyoyin kasar.

A cewar jaridar Vanguard, masu bada hasken shari’a a ranar Juma’a 23 ga watan Satumba, sunce kafin kasa tayi yunkurin siyar da dukitoyinta, abu na farko da gwamnati ke bukatar yi shine ta “dauki kaya na kudi- nawa muke bukata?”

Yace abu na biyu da zata yi shine “ tunanin abun bukata- A ina muke bukatar sa kudin? Neman sani a kan haka zai ba gwamnati haske.”

KU KARANTA KUMA: Anyi wa ma'aurata wanka da ruwan acid

Agbakoba ya shawarci shugabn kasa Buhari da ya yi koyi da tsarin Obama kan koma bayan tattalin arzikin Amurka ta hanyar shawarwari ga majalisar dokoki da kuma maida doka na karfafa tattalin arziki cikin gaggawa

A halin yanzu, Sanata dake wakiltan jihar Kaduna ta tsakiya Shehu Sani ya bayyana cewa dukkan wadanda ke kira ga sayar da dukiyoyin kasa saboda koma bayan tattalin arziki a matsayin ‘marasa tausayin tattalin arziki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel