Wadan nan jaruman sun kashe katon maciji

Wadan nan jaruman sun kashe katon maciji

Wasu mutane sadauka ne, suna da karfi da kwazon yin wani da wasu ba za su yi ba.

Mutane kalilan ne wadan da suke yin tunani mai zurfi kafin suyi wani abu, d da yake yawanci basu cika yin hakan ba, su fahimci amfanin yin wani abu musamman ana so ayi shi da gaggawa.

Amma dole mu fahimci cewa mutane suna fahimtar abubuwa dai-dai da tunanin su, sai dai wasu suna da jarumtakar samun warakar abun da ya faru, wasu kuma zasu kasance cikin tsoro wanda b ze basu damar yin tunani ba.

Wannana haka yake tunda akwai sinadarai a cikin jikin mu mai sa muyi tunani, gudu ko tashi ko muyi wani abu akai ko muji tsoro. Dan haka in ka ga mutane suna gudu in suka fada wa hatsari, wannan shine hanyar da tunanin su ya basu dan guje ma hatsarin, wasu kuma zasu yi kokarin neman kare kai, amma yawancin mutane sun fi jin tsoro.

Wasu matasa 2 a jahar Akwa Ibom sun burge, sun samu damar kashe katon maciji kuma basu ji tsoron yin haka ba, zasu yi farin cikin nuna abunda suka yi duk da ya Ke abun be wuce ya kare a tukunyar miya ba.

Kasan cewar kowa ya san yadda tattalin arziki yake a yanzu, dan haka wadan nan samarin suna cikin sha'ani dan basu da bukatar sayen nama ko kifi a kwanaki kusa masu zuwa, kashe katon maciji ya nuna zasu iya jarumta gurin farauta in sun so gwada jarumtar su.

Kalli hotuna

Wadan nan jaruman sun kashe katon maciji
Wadan nan jaruman sun kashe katon maciji
Wadan nan jaruman sun kashe katon maciji

Asali: Legit.ng

Online view pixel