Labari da duminsa: Sojojin ruwa sun cafke wani jigon Avengers

Labari da duminsa: Sojojin ruwa sun cafke wani jigon Avengers

- Abraham Sule, wanda ake zargi jigo ne na Neja Delta Avengers ya fada hannun hukumar sojojin ruwa kusa da Sapele a jihar Delta

- An Kama Suru, wanda dan asalin jihar Ondo ne ranar Talata 20 ga Satumba kusa da Sapele inda yake buya

- Ya dai amince da zargin kasancewa dan tsagera da kuma hannu cikin fasa bututun mai da gas amma ya karyata zama mamba na Neja Delta Avengers

Labari da duminsa: Sojojin ruwa sun cafke wani jigon Avengers

Hukumar sojojin ruwa ta kama wani wanda an dade ana zarginsa da zama dan kungiyar tsagerun Neja Delta Avengers a kusa da karamar hukumar Sapele ta jihar Delta, cewar jaridar The Punch.

Rohoton na cewa, an dai kama Abraham Suru, wanda kuma ake kira da Gabon makwanni bayan hukumar soja tayi tallar nemansa akan zargin yana da hannu cikin barnar da ake ma cibiyoyin mai da iskar gas a kananan hukumomin Warri ta yamma da kudu maso yamma na jihar. An kama Suru, wanda dan asalin jihar Ondo ne ranar Talata 20'ga Satumba kusa da Sapele inda yake buya.

KU KARANTA: ‘Yan Shi’a sun sha barkonon tsohuwa a Abuja

An fadi haka ta bakin kwamandan jirgn ruwa mai suna Delta Commodore Joseph Dzunve lokacin da ake nuna wanda ake zargi ga masu daukar labarai a sansanin sojan ruwa na Warri. Commodore Dzunve yace anci nasarar kama Gabon bayan hukumar sojojin ruwa ta dade tana nemansa da kuma taimakon samamen da suke kaiwa mai suna Operation Delta Safe koko tabbatar da lafiyar Delta mai kokarin fatattakar tsageru da masu laifi daga yankin. Ya ci gaba da cewa:

"A kokarin gwamnatin tarayya na hana satar danyen mai da sauran ayyukan barna a cikin gulabe da tafkunan kasar, jirgin yakin sojan ruwa mai suna Delta wanda ke cikin rundunar  Operation Delta Safe koko tabbatar da tsaron Delta ta kama wani sannanen shugaban gungun dake barna tun cikin 2011. Shi (Abraham Suru koko Gabon) nada hannu cikin fasa bututun mai, fashi da makami, fashin jiragen ruwa, satar mai, ana kuma zarginsa da kasancewa mamba na  Neja Delta Avengers."

Dzunve, ya kara da cewa, Gabon shugaba ne na wani bangaren tsagerun Neja Delta Avengers wanda a cikin mambobinta akwai janar Felix wanda tun tuni jami'an suka cafke shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel