Budurwar da ta zama Shugaba a Arewacin ta shiga Ofis

Budurwar da ta zama Shugaba a Arewacin ta shiga Ofis

- Budurwar nan da aka nada Shugabar Karamar Hukuma a Arewacin Najeriya ta shiga Ofishin ta

- A jiya, Alhamis, 22 ga watan Satumba dai Hindatu Umar ta dare kujerar shugabar karamar hukumar Argungu dake jihar Kebbi

– Mutanen Arugungun suna gani cewa ba ta dace ta shugabanci karamar hukumar ba

Budurwar da ta zama Shugaba a Arewacin ta shiga Ofis

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

BBCHausa ta rahoto cewa Buduwar nan da muka kawo labarin ta kwanaki da suka wuce ta shiga ofis. A ‘yan kwanaki da suka wuce ne dai aka nada wata Budurwar mai suna Hindatu Umar a matsayin Shugaban Karamar Hukumar Arugungun dake Arewa maso Yammacin Jihar Kebbi. An nada wannan budurwa ne bayan wa’adin kwamitin rikon kwaryar da aka nada ya kare.

A dai Ranar Allhamis, watau Jiya, Hindatu ta dare kan kujerar ta ta Shugaban Karamar Hukumar Arugungun, Karamar Hukumar Arugungun dai tana daga cikin Manyan Kananan Hukumomin Jihar. Rahotanni sun nuna cewa an nada Hindatu Umar ne a matsayin Shugabar Karamar Hukumar bisa umarnin Gwamnatin Jihar. Kamar dai yadda muka bayyana a baya, An nada wannan budurwar ne bayan wa’adin kwamitin rikon kwaryar da aka nada ya kare.

KU KARANTA: An nada Yarinya mai shekaru 25 a matsayin Shugaba a Arewacin Najeriya

Ko a lokacin da wancan tsohon Shugaban yake kan mulki, an ce Malama Hindatu ce mataimakiyar sa. Sai dai mutanen Argungun sun koka da nadin na ta, a cewar su, ita ma ya kamata ta sauka daga mulkin tare da wancan tsohon Shugaban da wa’adin za ya kare.

Dam dai can Mutanen Arugungun basu goyi bayan nadin na ta ba, domin kuwa ba a taba samun mace da zama Shugaba haka a Tarihi ba. Sun kuma koka da cewa ban da cewa mace ce, tana da karancin shekaru, sannan kuma ba ta san harkar Shugabancin Karamar hukuma ba ko kadan, ga shi kuma ba ta da wani zurfin karatun boko.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel