Dangote zai siya kungiyar Arsenal

Dangote zai siya kungiyar Arsenal

Shahararren attajirin nan dan kasar Najeriya Aliko Dangote ya shirya tsaf don siyan fitacciyar kungiyar kwallon kafa ta Arsenal a cikin shekaru hudu masu zuwa.

Dangote zai siya kungiyar Arsenal

Dangote ya nuna sha’awar siyan kungiyar ne sakamakon rashin samun nasarar lashe kofina iri iri da kungiyar bata yi, masana sun kiyasta arzikin Dangote a shekara ta 2015 da ya kai kusan pan biliyan 8.3.

Dangote ya bayyana ma jaridar Bloomberg cewa “wata kila nan da shekaru uku ko hudu, muna fuskantar matsaloli dangane da cinikin, don haka dole sai an warware matsalolin tukuna kafin musan halin da muke ciki, daga nan sai in fuskanci maganar.” A shekarar bana, Dangote yayi asarar makudan kudade da suka kai pan miliyan 3.3 sakamakon karyewar darajar naira.

KU KARANTA: Dangote zai sake gina asibitocin Yobe

Dangote ya kara da cewa “ba wai zancen mu siya Arsenal bane, kuma a ci gaba da halin da ake ciki, a’a. burin mu shi ne mu siya Arsenal, kuma mu canza akalar ta, na tafiyar da kasuwanci na cikin nasara sosai, don haka ina ganin zan iya tafiyar da kungiyar Arsenal ma cikin nasara. “amma sakamakon ayyukan dake gaban mu a yanzu da suka kai na dala biliyan 20, ba zan iya raba hankalina ba.”

Kungiyar Arsenal ta dade tana da matsaloli daga mutumin dake da kaso mafi tsoka na kungiyar Stan Kroenke wanda hakan ya sanya kungiyar ta kasa siyan manyan yan kwallo.

Kimanin shekaru 12 kenan rabon da Arsenal ta lashe gasar cin kofin firmiya, sai dai kungiyar tayi kokarin lashe gasar cin kofin kalubale sau biyu a wannan tsakan kanin. A karshen kakar bane ne magoya bayan kungiyar suka yi korafin a cire mai horar da Arsenal, Arsene Wenger tare da Stan Kroenke wanda ke mallakan kasha 67 na kungiyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel