An tsinci gawar dan Najeriya a lungun tayar jirgin Saudi

An tsinci gawar dan Najeriya a lungun tayar jirgin Saudi

Wani abin al’ajabi ya faru yayin da ake duba wani jirgin sama mallkan wata kamfanin jirage na kasar Saudiya daya dawo daga Najeriya a filin tashin jirage na tunawa da Sarki Abdulaziz lokacin da aka tsinci gawar mutum.

An tsinci gawar dan Najeriya a lungun tayar jirgin Saudi

Shi dai jirgin mallakan kamfanin Flynas dawowarsa kenan daga Najeriya inda yaje mayar da mahajjata gida bayan sun kammala aikin hajji, a lokacin da ma’aikatan kamfanin ke duba lafiyar jirgin ne sai suka ci karo da gawar wani mutum a cikin lungun da tayar jirgin ke makalewa a ranar laraba 21 ga watan satumba.

KU KARANTA: Alhazan Najeriya 18 suka rasu tal-in-tal a hajjin bana

Jaridar Saudi Gazatte ta ruwaito cewa “da misalin karfe 12 na rana ne, muka tsinci gawar wani bakin mutum a lungun da tayar jirgi ke makalewa.” Ana tunanin mutumin ya shiga lungun tayar ne don samun damar shiga kasar Saudiya a boye, sai dai bay au aka saba yin irin haka ba, saboda mutane da dama sun mutu ta wannan hanyar.

An tsinci gawar dan Najeriya a lungun tayar jirgin Saudi

Rahoton ya bayyana cewa tuni kamfanin ta tuntubi hukumar da ta dace kan maganar. Sai dai, kusan duk shekara tun 2009, sai an samu akalla mahajjata 10 dake rasuwa. Ana yawan samun hadaruruka a yayin aikin hajji, don haka ne ma malamai suka bukaci mahajjaci ya rubuta wasiyya ya ajiye.

Asali: Legit.ng

Online view pixel