Man utd da Man city zasu sake karawa a gasar EFL

Man utd da Man city zasu sake karawa a gasar EFL

- Manchester United da Manchester City zasu sake karawa a zagaye na hudu don neman cin kofin EFL.

- Chelsea zasu hadu da West-Ham a wasan gaba a birnin Landan bayan da dukkannin kungiyoyin suka samu nasarar tsallakewa a wasan zagaye na gaba.

- Wani wasan mai zafi kuma zai gudana ne a tsakanin Tottenham da Liverpool a Anfield.

Manchester zasu kara karawa, inda Manchester United da Manchester City zasu kara karawa a wasan zagaye na hudu na kokarin cin kofin EFL.                               Hankalin Mourinho ya kwanta, inda United din ta samu nasarar lallasa kungiyar Northampton daci 3-1 a wasan zagaye na uku da suka buga a filin wasa na Sixfields.

Pep Guardiola wanda shine kochin Manchester City, kungiyar tashi ta sami nasarar tsallakewa zuwa zagaye na gabane bayan da suka lallasa takwaransu da suke buga gasar firimiya wato Swansea City daci 2-1.

Man utd da Man city zasu sake karawa a gasar EFL

Wannan babbar haduwar nasu shine zai kasance haduwar su na biyu wanda kocin kungiyoyin biyu sukeji da kansu a duniyar kwallon kafa, bayan da kungiyoyi zasu sake karawa a karo na biyu cikin dan wannan tsakanin.

Wani kuma wasan mai kayatarwa shine wasan da zai guda a birnin Landan, inda Chelsea zata kara da West-Ham, bayan da kowa yake ganin damar kowa.             Sannan kuma Tottenham zata ziyarci Liverpool a Anfield.

Antonio Conte, zai kasance a wajen layin filin buga wasan da zai gudana tsakaninsu da West-Ham a zagaye na hudu dan neman cin kofin EFL.

Man utd da Man city zasu sake karawa a gasar EFL

Mutanen Conte dai sun sami nasarar kara sama kungiyar kwallon Leicester kwallaye 2 daga baya a inda wasan ya kare daci 4-2. Sai kuma Liverpool da Tottenham suka samu nasarar cire abokanan hamayyar su, wa'anda basu buga gasar firimiya.

A wasan gabar daya gudana dai a kwanakin baya na manchester, ya karene inda City ta doke United daci 2-1, inda De Bruyne da Kelechi Iheanacho suka sami damar zurama kungiyar nasu kwallaye, sai kuma daga baya Zlatan Ibrahimovic ya cima United kwallo daya. Inda wasan ya kare City ta doke United daci 2-1 a Old Trafford.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel