Rundunar Sojan ruwa ta mallaki gagarumin jirgin yaki

Rundunar Sojan ruwa ta mallaki gagarumin jirgin yaki

Cikin cigaba da kyautatawa tare da inganta tsaro, gwamnati ta saya ma rundunar sojan ruwa gagarumin jirgin yaki.

Rundunar Sojan ruwa ta mallaki gagarumin jirgin yaki
Jami'an sojan ruwa a gaban jirgin

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa an kammala kera jirgin yakin nan mallakan sojin ruwa mai suna NNS Unity, a yanzu haka yana kan hanyarsa ta isowa Najeriya.

Shugaban sashin tsare tsare na rundunar Rear Admiral Jacob Jani ne ya wakilci babban hafsan sojan ruwa Abubakar Sadiq a wajen amsan jirgin yayin da zai kamo hanyar Najeriya. Ajani ya mika godiyar daukacin rundunar sojan ruwa ga shuagban kasa Muhammadu Buhari daya bada izinin kammala kerawa tare da shigo da jirgin.

Ajani ya bayyana kasancewar jirgi NNS Unity cikin jerin jiragen sun a yaki zai kara ma jami’ansu kwazon kawar da duk wasu miyagun aikace aikacen da mwasu bata gari ke aikatawa a kan ruwan kasar, da yankin kasar Guinea.

KU KARANTA:Karon batta tsakanin dan ‘union’ da sojan ruwa

Ya kara da cewa, rundunar zata fara shiga ireiren wuraren da bata iya zuwa sintiri sakamakon mallakar jirgi NNS Unity wanda zai kara ma rundunar kaimin fuskantar matsalolin tsaro da suka addabi gabobin ruwan kasar nan. sa’anan jirgin yaki NNS Unity zai yada zango a wasu tashohin ruwan kasashen kawancen Najeriya, inda yace hakan zai kara dankon zumunci tsakanin kasashen. Ajani ya karkare jawabinsa da mika kokon barar ganin kyakkyawar dangantakar dake tsakanin Najeriya da kamfanunuwa masu kera jirage a kasar Sin ya daure.

An bayyana taron mika jirgin yakin ga Najeriya a matsayin nasara ga Najeriya, taron ya samu halartan shugaban kwamitin sojin ruwa a majalisar dattijai Sanata Isa Misau, shugaban kwamtin sojan ruwa a majaliasar wakilai Abdulsamad Dasuki, wakiliyar ministan tsaro Hajia Rabi Tedman.

A yanzu haka Jirgin yaki NNS Unity ya nufo Najeriya tun bayan tasowarsa daga kasar Sin a ranar Juma’a 16 ga watan Satumba, inda ake sa ran zai iso Najeriya a satin farko na Nuwamba shekara ta 2016.

Asali: Legit.ng

Online view pixel