Fastocin Anglican sun tsere gabanin zangazangar Biafara

Fastocin Anglican sun tsere gabanin zangazangar Biafara

An karkare wani taron kara ma juna sani na kwanaki biyar da kungiyar Fastocin Anglican ta shirya ba shiri sakamakon zanga zanga da kungiyar tabbatar da kasar Biafara (IPOB) zata gudanar a yankin kudu maso gabashin kasar nan.

Fastocin Anglican sun tsere gabanin zangazangar Biafara
Shugaban cocin Anglican Nicolas Okoh

Ita dai kungiyar IPOB ta sanar da ranar 23 ga watan satumba a matsayin ranar zanga zangar inda ta bukaci kada wani ya fita a ranar, sa’nnan kada wani ya bude shago ko yawon kasuwanci.

Jaridar Vanguard ta ruwaito kungiyar Fastocin Anglican tana gudanar da wani taro ne da ya samu halartan Fastoci 170 wanda kuma zai kare a ranar Juma’a, sai dai ba shiri suka rufe taron a ranar Laraba saboda zanga zangar.

Shugaban kungiyar Fastocin Anglican Rabaren Nicolas Okoh ya roki kungiyar IPOB data sassauta dokar nata, saboda hakan zai shafi shirin tafiyarsu zuwa garururwansu.

Kungiyar IPOB tayi barazanar rufe kasuwanni da saurana wuraren aiki, tare da sanya dokar hana fita a gaba daya yankin kudu maso gabas. Ba ruwanmu da rigimarsu, amma muna rokan su dasu bari har sai mun bar garin Awka ranar Juma’a kafin su fara zanga zangar.

KU KARANTA: Wani Matashi ya damfari Bishop Oyedepo,Dantata da sauransu

Idan ko ba haka ba, zanga zangar zata tadda mu a gadar Neja don kuwa itace kadai hanyar da yawanci Fastocinmu zasu bi domin fita daga jihar Anambra, muna rokon jama’a dasu taya mu rokon su, inji shi.

Duk da cewa ba’a dade da fara taron ba, amma ya zaman ma Fastocin dole su rufe taron don gudun fadawa cikin rikicin dokar kungiyar IPOB. Daya daga cikin Fastocin daya fito daga yankin Arewa ya bayyana damuwarsa da zanga zangar “mu ma mutane ne, don haka ne muka yanke shawarar rufe taron. Wannan shi ne abinda yafi kamata muyi dama. Da yamman nan zan fita, sauran abokaina ma haka, wasu kuma zasu tafi gobe da sassafe, babu amfanin jira.

Asali: Legit.ng

Online view pixel